Hukumar zabe ta kasa INEC, ta sanar cewa ta kafa kwamiti don gudanar da bincike kan korafe –korafen da ake yi cewa yara kanana sun kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da aka yi a jihar Kano.
Shugaban hukumar Mahmoud Yakubu ne ya sanar da haka inda ya kara da cewa kwamitin mutum shida din da hukumar ta kafa zai gabatar da sakamakon binciken sa nan da makonni biyu.
“Babu ruwan kwamitin da binciken sakamakon zaben da aka yi amma za ta bankado mana gaskiyar abin da ya faru ne game da cece-kucen da aka yi ta fama da shi cewa wai wadanda basu kai shekarun zabe ba sun kada kuri’a a Kano.
Ya ce hukumar zabe a shirye take don inganta aiyukan zabe a kasar nan.