Ya kamata Buhari ya jagoranci zanga-zangar wahalar mai a kasar nan, inji Sule Lamido

0

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari da babban jigon APC, Bola Tinubu gwalo da shagube, dangane da matsalar man fetur da kuma yaki da cin hanci da rashawa, inda ya nemi a yanzu ma ai babu wanda ya hana su fitowa yin zanga-zanga.

Da ya ke jawabi a wurin Taron Shekara-shekara da Kamfanin Jaridar Daily Trust ke shiryawa, na 2017, Lamido ya ce, “Bola Tinubu ya kasa halartar taron ne saboda motar san a can a kan layin sayen fetur a gidan mai a Lagos. Layi bai kai ga zuwa kan motar Tinubu ba, ballantana ya sha mai ya zo wurin wannan taron a Abuja.” Inji Sule Lamido.

Lamido ya kuma dora alamar tambaya a kan yadda wannan gwamnatin ke yaki da cin hanci da rashawa.

Lamido ya fakaice da guzuma ya harbi karsana, inda ya yi maganar rawar da Buhari ya taka a karkashin mulkin Abacha, wanda ya ce cike ya ke harkalla da harankazamar satar kudade.

“Kwanan nan Attoni Janar ya kammala sa hannun dawo da karin wasu kudi da Abacha ya sace, amma nan wani ya fito kiri-da-muzu ya ce Abacha bai sace ko sisi ba.” Inji Lamido, wanda kowa ya san da Buhari ya ke, domin shi ne ya furta cewa Abacha bai saci ko sisi ba, a farkon shekarar da ta gabata.

Share.

game da Author