Kwamishinan harkokin mata na jihar Kaduna Hafsat Baba, ta sanar cewa gwamnatin jihar ta ware naira miliyan 200 domin tallafa wa mata a jihar.
Hafsat ta ce bayan wannan shiri da gwamnati ta yi ma’aikatar ta ta gina wauraren koyon sana’a wa mata a jihar har guda uku domin koyar dasu sana’ar hannu.
Bayan haka ta ce da zaran ma’aikatar ta ta kammala shirya ka’ido’jin da duk mai bukatar bashin zai cika kafin ya samu, za ta sanar wa mutane domin su fara karba.
Daga karshe ta ce wannan wuraren koyon sana’a zai taimaka wa ba mata ba kawai har da matasa dake sun inganta rayuwar su.
Discussion about this post