Amfanin sinadarin ‘Iodine ‘ ga mace mai ci

0

Wasu likitoci daga cibiyar gudanar da binciken lafiya dake kasar Amurika NIH sun bayyana cewa rashin isasshen sinadarin ‘Iodine’ a jikin mace na hanata iya daukar ciki.

Likitocin sun gano haka ne a sakamakon binciken da suka gudanar kan matsalolin da ka iya hana mace daukan ciki.

Wadanda suka jagoranci wannan bincike James L. Mills da Eunice Kennedy Shriver sun bayyana cewa bayan taimakawa wajen daukar ciki da wannan sinadarin na ‘Iodine’ ke yi yana kuma taimaka wa wajen girma da bude kwakwalwan jaririn dake ciki da kara masa kwarin kashi.

Likitocin sun kara da cewa rashin isasshen wannan sinadari na ‘Iodine’ a jikin macen dake neman haihuwa na iya hana ta daukar ciki sannan rashin sa ga mata mai ciki na iya sa a haifi da musaki ko kuma gajiyayyen dan da bashi da kwari.

Daga karshe likitocin sun yi kira ga masu ciki da su yawaita cin abincin dake dauke da sinadarin ‘Iodine’ kamar su madara musamman madaran akuya, kifi, amfani da gishirin da ake kira ‘Iodized salt’ wajen girka abinci, dankali na turawa da hausa da sauran su.

Share.

game da Author