SHAWARA: Za ayi wa mutane miliyan 3 rigakafi a jihar Zamfara

0

Kwamishinan kiwon lafiyan jihar Zamfara Lawal Liman ya bayyana cewa za su yi wa mutane miliyan 3.2 allurar rigakafin cutar shawara wato ‘Yellow Fever’ a jihar.

Ya fadi haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau inda ya kara da cewa za su yi alluran ne da hadin guiwar hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na kasa.

Liman ya kara da cewa suna sa ran yi wa mutane ‘yan watani tara zuwa shekaru 45 alluran a jihar sannan suna kira ga mutane da su bada hadin kai.

Share.

game da Author