Daya daga cikin mutanen da jami’an tsaro na SARS suka dirka wa bindiga a Jos, ya mutu, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar.
An yi harbin ne a wata mashayar barasa a Dorawa, kusa da Makarantar Koyon Fasahar Aikin Asibiti, a cikin karamar hukumar Jos ta Kudu.
Wanda aka harba din mai suna Henry Anthony, ya mutu da misalin karfe 8 na dare a ranar Alhamis da dare, kamar yadda kawun sa mai suna Victor Dokotri ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Dokotri ya ce da gangan jami’an tsaron suka dirka wa dan nasa bindiga, ba a kan kuskure ba ne.
“Karya suke yi da suka ce wai harsashi ne ya subuce ya same shi.
‘‘Abokin sa da aka yi komai a kan idon sa, ya ce mana Dokotri da Samuel abokin sa da wata mata mai suna Margaret su na tare su uku, sai SARS suka kai musu samame.
Ya ce dama kawai su na kai samame ne a wata mashayar da suka same su, mai suna Congo da ke Dorawa.
A karshe dai ya ce ba su yafe ba, za su kai maganar a gaba, domin a bi wa mamacin hakkin sa a kan ’yan sandan.
Discussion about this post