APC ta kama hanyar jam’iyyar shiririta – Hon. Dogara

0

Kakakin Majalisar Tarayya, kuma daya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar APC, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa tun daga jam’iyyar APC kanta, da sauran jam’iyyu, ba su da wani sauran katabus din jaddada ingantacciyar dimokradiyya.

Dogara ya ce jikin jam’iyyun duk ya yi laushi, sannan kuma sun kama shiririta, musamman APC da ba ta da tasirin kafa ginshikin siyasar cikin gidan ta mai kwarin gaske.

Ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron da Cibiyar Nazarin Tsarin Tafiayar da Mulki, da ke Jos ta shirya a Abuja.

Dogara, wanda Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Tarayya, Yakubu Umar Barde ya wakilta, ya ce a kokarin da jam’iyyun siyasa ke yi domin su dawwama a kan mulki, sai su rika yi wa jama’a alkawurran karya domin cimma manufar su.

Share.

game da Author