Duk da barazanar bijirewa dokar hana kiwata dabobi a fili da makiyaya suka yi dokar fara aiki a jihar Taraba ranar Litini.
Gwamnan jihar Darius Ishaku ya ce duk da wannan barazana dokar ta zo ta zauna daram-dam a jihar.
Mai taimaka wa gwamnan kan harkar yada labarai Emmanuel Bello ya sanar da hakan inda ya kara da cewa yayin da gwamnati ke kokarin kirkiro wuraren da makiyayan za su kiwata dabbobin su, gwamnati za ta kafa dokar ne a hankali domin makiyaya su saba.
Ya ce sun kuma shirya taron wayar da kan masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin jihar a Jalingo wanda za a fara ranar Alhamis sannan za su fara horas da jami’an tsaron da za su tabbatar da an bi dokar sau da kafa.
Bayan haka Ishaku ya ce ya gana da sarakunan gargajiya ranar Litini da ya gabata inda suka ware wuraren kiwata dabbobi a killace a mazaba uku a jihar wanda za su fara aiki cikin kwanakin nan.
Daga karshe a ranar Laraba shugaban kungiyar makiyaya ‘Dandalin Makiyaya Cattle Breeders of Nigeria DMCBN’ Umar Bello ya shaida wa gwamnati cewa hana su kiwata dabbobinsu a filli ba tare da samar musu da wani wurin ba zai yi matukar wahala basu bijire wa wannan doka ba.
Ya kuma ce kama su da gwamnati ke kokarin yi don wannan doka ba zai haifar da komai ba illa rikici a jihar.