Obasanjo ne zai kushe Buhari, bayan shine abin ki, mu dai Buhari mu ke yi – Uzor Orji Kalu

0

Tsohon gwamnan jihar Abia, Uzor Orji Kalu ya bayyana cewa wasikar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari wasika ce da baza tayi wani tasiri ga ‘yan Najeriya.

Kalu ya fadi haka ne da ya ke zantawa da manema labarai a filin Jirgin saman Murtala Muhammed dake Legas.

Ya ce Buhari ya yi abin azo a gani musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa wanda yayi kaurin suna lokacin mulki PDP.

” Buhari yayi abin  yabawa a cikin shekaru biyu da rabi da yayi yana mulki a kasar nan.

” Ina ganin wasikar Obasanjo ba yayi ta bane don ci gaban Najeriya, saboda haka ba yanzu bane zan bashi amsa.

” Mu dai a yankin kudu dole mu yaba wa Buhari domin kuwa a lokaci da Obasanjo ke mulki bai waiwayi gadar ‘Second Niger Bridge’ ba amma gashi yanzu Buhari ya fara aiki akai.

” Obasanjo bai gina mana titin ‘Port Harcourt-Okigwe-Umuahia-Enugu ba amma gashi Buhari na yi mana.

Sannan akwai titin Enugu-Awka-Onitsha da titin Onitsha-Owerri-Aba wanda a shekaru takwas da Obasanjo yayi bai yi su ba sai yanzu da Buhari ya  hau ake yin su.

” Tsakani da Allah idan zan zabi masoyi wa zan zaba? Buhari zan zaba, kuma shi zan bi ya shugaban ce ni.”

Sannan kuma ya tunatar da Obasanjo irin watanda da akayi da dala Biliyan 16 na gyaran wutan lantarki a kasar nan wanda har ya gama mulki ba a samar da wutan ba sannan ba ace ga inda kudi suke ba.

Kalu ya ce zai ba Obasanjo ansa idan ya dawo daga tafiyar sa.

Share.

game da Author