2019: Kungiyar ’yan kasuwa ta goyi bayan Buhari ya tsaya takara

0

Kungiyar ’Yan Kasuwa ta goyi bayan sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a 2019. Haka Shugaban Kungiyar, Bature Abdul’aziz ya bayyana wa manema labarai a Kano, jiya Alhamis.

Ya bayyana cewa dalilin su na goyon bayan sake zaben sa da kungiyar ta yi, ya zo ne saboda yakinin da suke da shi cewa Shugaba Buhari zai kara kai kasar nan zuwa gacin zama hamshakiya mai dimbin yalwa da ingantaccen tattalin arzikin kasa.

Sun kuma nuna farin ckin irin nasarori da ci gaba da aka samu a cikin shekaru biyu da rabin din yanzu da Buhari ya yi a kan mulki.

Kungiyar ta kuma gamsu da yadda aka samu nasarar karya karfin Boko Haram da kuma yaki da ake yin a kashe cin hanci dacrashawa a kasar nan.

Share.

game da Author