Tun cikin 1978 na fara fahimtar inda aka fara samun matsala a tsakanin Fulani makiyaya da kuma manoma. A lokacin ina karami a kauye, idan kaka ta yi, yawancin manoma su kan ki kwashe amfanin gonar su da wuri. Za su tattara shi wuri daya a cikin gona, amma ba za su kwashe su kai gida ba.
Maimakon haka, sai su tattara gero, dawa ko gyada a wuri daya a tsakiyar gona, su yi zabaro na karan dawa ko karan gero su rufe.
Wasu matasan kauye za su tara amfanin gonar na su a gona, su rufe, sai su fantsama cikin garuruwa yawon ci-rani. Haka za a dauki tsawon lokaci, har rani ya shigo lokacin da ya kamata a fara sakin dabbobin gida irin su akuya, tunkiya da jakai su na fita daji kiwo sakaka, ba tare da makiyayi tare da su ba.
Kafin wannan lokaci, Dagatan kauye da masu Unguwanni kan sa a yi yekuwa ana tunanar da manoma cewa kowa ya kwashe amfanin gonar sa, domin za a bada umarnin a saki dabbobi su fita kiwo, saboda rani ya yi, abincin dabbobi ya fara karanci.
To daga karshe kuma sai a yi yekuwar bada umarnin a saki dabbobi su fita kiwo, sakaka, ba tare da wani makiyayi na biye da su ba:
YEKUWA:
“Sarki ya aiko ni,
Hakimi ya aiko ni,
Maigari ya aiko ni,
Abin da su ka ce a fada muku jama’a,
Duk daukacin magidanci duka,
Idan Allah ya tashe mu gobe lafiya,
Da mai akuya da mai saniya da mai tunkiya,
Kowa ya balle bisashe nai.”
Watau wannan ballewar ta na nufin a balle dabbar ka daga tirke, ka sake ta ta rika fita jeji da gonaki ta na kiwo da kan ta, ba tare da makiyayi ba. Za a saki akuya ko tinkiya su rankaya jeji su na kiwo. Idan rana ta take tsaka wajen daya na rana, za su dawo gida su sha ruwa, kuma su koma jeji kiwo. Daga nan ba za su koma ba, har sai rana ta fara disashewa, magriba za kusa, sannan za su koma gida, a kama kowace, a daure, sai kuma gobe da safe.