Abinda El-Zakzaky ya fadi wa manema Labarai

0

A karon farko, shugaban mabiyan Shi’a na Najeriya, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya bayyana a gaban ‘yan jarida, inda aka nuni shi ya yi wani takaitaccen bayani.

Hukumar Tsaro ta DSS ce ta gayyaci wasu daidaikun ‘yan jarida inda ta gabatar musu da malamin a cikin harabar ofishin hukumar da ke Aso Drive, Abuja.

Gidan talbijin na Channels ya nuno El-Zakzaky daure da rawani, ya na sanye da gilashi sannan kuma an daura masa katon bandeji a wuyan sa, wanda ya tallabe masa wuya da kasan habar gemun sa.

Ba a gayyaci PREMIUM TIMES ba, don haka ba za mu iya tantance yadda yanayin lafiyar sa ta ke ba.

Ya bayyana ne, kwanaki uku bayan da aka fara yada rudun cewa ya mutu. Wannan zai iya sanyawa shi ne dalilin da ya sa aka nuna shi domin a tabbatar da cewa ya nan da ran sa bai mutu ba.

Jim kadan bayan takaikataccen bayanain da ya yi wa ‘yan jarida a cikin harabar ginin DSS, sai ya shiga mota kirar PRADO JEEP SUV, aka yi gaba da shi.

A cikin jawabin da ya yi, ya bayyana cewa ciwon na sa ya tsananta ne ranar Litinin, amma daga baya sai ya fara samun sauki. Ya ce a karon farko a wannan lokacin an kyale likitocin sa sun duba shi.

“A wannan karon likitoci na ne su ka duba ni, ba likitocin jami’an tsaron gwamnati ba.

“Yanzu ina samun sauki, ina kuma godiya da irin addu’o’in da ku ke yi min.”

Da ya ke maida raddi dangane da nuna malamin, kakakin IMN masu gwagwarmaya, Ibrahim Musa, ya ce su ma ba a gayyace su ba, sai dai gani suka yi an nuno shi a talbijin.

Daga nan sai ya kara shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba nuno malamin na su a talbijin ne ya dame su ba. Abin da su ke bukata shi ne a sake shi kawai ya fita ya nemi magani, kamar yadda kotu ta bata umarni tun cikin 2016.

Share.

game da Author