Gwamnoni sun zargi NNPC da karkatar da makudan kudade

0

Kungiyar Gwanonin Najeriya, NGF, ta bayyana cewa kamfanin man fetur na kasa, NNPC, ya shafe shekara biyar kenan cur ya na karkatar da makudan kudaden da ba a san inda ake boye su ba.

Kungiyar Gwamnonin ta ce kudaden da NNPC ke karkatarwa dai ba ta zuba su a asusun tara kudaden shiga na Gwamnatin Tarayya.

Ta fara buga misali da lokacin da gangar danyen man fetur ta kai har dalar Amurka 110, amma kuma yawan adadin kudin da NNPC ke Tarawa, kwata-kwata bai kai alamar yawan danyen man fetur din da Najeriya ke sayarwa a kasashen waje ba.

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa ne, kuma Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ya bayyana haka ga manema labarai yau Juma’a, inda ya kara da cewa sun tayar da wannan batu a taron da suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari, domin ya san halin da ake ciki.

Share.

game da Author