Shugaban hukumar kare hakkin mutane da ingancin abinci‘CPC’ Babatunde Irukera ya ce sun kammala shirye shirye tsaf wajen kafa dokar kare hakin marasa lafiya a asibitocin kasar nan da ake kira ‘Patient’s Bill of Rights’.
Ya ce dokar za ta taimaka wajen wayar da kan mutane musamman marasa lafiya da malaman asibitocin kasar nan wajen Samar musu kariya daga wulakancin wasu ma’aikatan asibitoci da sauran su.
Irukera ya ce yanzu haka kungiyar likitocin Najeriya NMA da sauran kungiyoyin ma’aikatan asibiti sun tabbatar musu cewa za su basu goyan baya don samun nasarar kafa wannan dokar.