‘Yan fashi sun kashe ‘yan sanda biyu a babban titin Akwanga zuwa Keffi

0

A yau ne jami’in dake Kula da harka da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa Kennedy Idrisu ya sanar da kisan gillan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan sanda biyu a babbar titin Akwanga-Keffi dake jihar.

Ya yin da yake zantawa da manema labarai a Lafiya Idrisu ya ce sun sun kafa shingen tsaro ne a kauyen Kubere dake kusa da babbar titin Akwanga-Keffi saboda yawan sace-sacen mutane da fashi da ake yi a wannan hanya me.

” Yayin da suke aiki ne a wannan wuri wadannan ‘yan bindigan suka far musu inda suke kashe ma’aikatan mu biyu.”

Ya ce yanaso ya tabbatar wa ‘yan ta’addan cewa hakan da suka yi ba zai da su dai na aikin da suke yi ba musamman yanzu da kwamishinan ‘yan sanda ya bada umurnin karo wasu ma’aikata zuwa hanyar.

Ya ce za su dage wajen sauke nauyin da ya rataya a kansu na kare rayuka da dukiyoyin jama’a musamman a wannan lokaci da ake shirin fara bukukuwan kirismeti.

Daga karshe Idrisu ya yi kira ga mutane yankin da su hada kai da ma’aikatan su don ganin sun kawar da masu aikata munanan aiyukka a wannan hanya.

Share.

game da Author