Shugaban kungiya mai zaman kanta ‘AIDS Healthcare Foundation AHF’ Kema Onu ta yi kira ga gwamantin da a shigar da wadanda suka kamau da cutar kanjamau cikin tsarin inshoran kiwon lafiya ta Kasa.
Kema ta bayyana haka ne a taron tunawa da cutar kanjamau da ake yi duk shekara a Abuja.
Ta Kara da cewa hakan zai rage wa gwamnati yawan kudaden da take kashewa wajen samar wa wadanda ke dauke da cutar kular da suke bukata.
‘‘Duk da hakan kamata ya yi Najeriya ta zage damtse wajen ware isassu kudade don hana yaduwan cutar’’.
Ta ce bincike ya nuna cewa mutane miliyan 3.2 ne suke dauke da cutar wanda 800,000 ne kawai daga cikin su ke samun kula sannan kungiyoyin bada tallafi na kasashen duniya na kula da 750,000 daga cikin su.