Shugaba Muhammadu Buhari ya ya tabbatarwa ‘yan Najeriya kokarin da gwamnatin sa ta ke yi na ganin ta farfado da tattalin arzikin Kasar nan.
Da ya ke magana a wajen bude wasu masana’antu biyu kafin kammala ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar Kano
ya ce alfanun tsarin zai haifar da samar wa dimbin matasa ayyukan yi da kuma kara inganta rayuwar al’umma.
Da ya ke kaddamar da masana’antar sarrafa mai ta Gezawa, Buhari ya yaba da mai kamfanin ta yadda ya dauko hanyar cin moriyar yanayin da kasar nan ke ciki, mai nuni da cewa duk wanda ya shuka hairan, to zai kwashi tulin adashen alheri.
Daga nan kuma sai ya bude masana’antar casar shinkafa da ke Kwanar Gunduwawa, kan titin zuwa Hadeja.
A nan ma ya jinjina kan yadda aka zabura wajen sake farfado da masana’antu Na cikin gida a kasar nan.
Mai kamfanin, Iro Gezawa, ya roki shugaban kasa da a sassauta tsauraran hanyoyi da matakan da masu son kafa masana’antun da suke da nasaba da harkokin noma ke bi kafin su samu isassun kudade.