Gwamnatocin Kaduna da Filato na kokarin ganin an sako Sango -Gwamna Lalong

0

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa ya jihar sa da Kaduna su na aiki tare domin ganin masu garkuwa da mutane sun sako Shugaban Jam’iyyar PDP na jihar, Damishi Sango.

An dai yi garkuwa da tsohon ministan wasannin ne tun a ranar Laraba a Jere, kan hanyar sa ta zuwa Abuja daga Jos.

Wadanda su ka yi garkuwar da shi sun nemi a ba su naira miliyan 80 kafin su sake shi.

Gwamnan ya ce ya fi kowa damuwa da garkuwar da aka yi da Sango, ya na mai cewa rashin tausayi ne, kuma rashin imani ne.

Daga nan sai ya yi wa iyalan wanda aka sacen jaje, har da jam’iyyar PDP, wacce Sango ke shugaban ta na jihar Filato.

Share.

game da Author