Fati Washa ta wake Gwaska, Zango ya yaba

0

Jaruma ‘yar wasan finafinan Hausa, Fati Washa ta bi sahun dubban masoya Adam Zango wajen tallata sabon fim din sa da ke gab da fitowa mai suna ‘Gwaska’ in da ta rera wakar kamar ita ta rubuta shi.

Fati ta baje gwazon ta ne a wata Bidiyo da ta yi sannan ta saka a shafinta na Instagram in ta wake wakar da farko har karshe in da shi kansa Zango sai ya yaba.

Gwaska dai fim ne da ba ataba irin sa ba a farfajiyar finafinan Hausa, saboda tsara shi da kayi da kuma irin abubuwan da akayi a fim din.

Zango ya sanar cewa zai gana da masoyan sa na Kano da ya hada da mata 15 maza 15 da suka fafata a gasar wakar fim din da ya sa a yi domin nuna wa kowa cewa alkawarin da ya dauka zai cika shi.

Share.

game da Author