Falana ya nemi Buhari ya saki El-Zakzaky da matar sa a dalilin rashin lafiya

0

Biyo bayan janye takardar korafin da ya yi kan Sojojin Najeriya, lauyan Shugaban Shi’a, Femi Falana ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gagauta sakin Elzakzaky tare da matar sa Zainab, a bisa dalilin lalura ta matsananciyar rashin lafiya.

“Elzakzaky tuni fa ya rasa ido daya na hagu, kuma a kusa ya ke da ya rasa daya idon na dama sanadiyyar azabtarwar da sojojin Najeriya suka yi masa. Bugu da kari kuma jami’an SSS sun hana shi fita waje domin ya nemi magani, kamar yadda likitocin cikin gida Nijeriya suka bayar da shsawara a yi.

“Hatta ma wata mafita da iyalan malamin suka bayar da shawara cewa a bari a shigo da likitocin ido daga kasar waje domin su yi masa aiki, ba a amince da hakan ba.”

Haka Falana ya bayyana a cikin wata sabuwar wasika da ya rubuta wa Buhari, inda ya yi kira da ya saki Elzakzaky da matar sa Hajiya Zainab.

Falana ya kara da cewa, duk da cewa matsalar El-zakzaky ta munana, to ta matar sa ta fi muni matuka.

“Ya na da kyau Shugaban Kasa ka sani cewa matsalar Zainab El-zakzaky fa ta fi ta mijin ta muni matuka. Amma saboda wasu dalilai jami’an SSS sun ki bari a cire wasu harsasai da ke cikin jikin ta tun bayan da aka bude mata wuta a ranar 14 Ga Disamba, 2015. Wannan ya sa a ko da yaushe ta ke cikin hali na matsancin fama da radadin ciwo a cikin jikin ta. Za a iya ceton ran ta ne kawai idan aka bari likitoci suka duba ta tare da yi mata magani.”

Ya ce ya yanke shawarar rubuta wa Shugaban Kasa wasika ne domin ya bada umarnin a sake su, ganin cewa gwamnatin tarayya ta ki bin umarnin kotun da ta ce a sake su tun a ranar 2 Ga Disamba, 2016.

Share.

game da Author