SABON SALO: Gwamnan Barno zai sa ’yan firamare da sakandare leken asiri

0

Gwamnatin Jihar Barno za ta fito da wata sabuwar dabarar yin amfani da daliban firamare da sakandare domin aikin liken asirin fallasa masu sace kayan abincin da ake bai wa daliban jihar.

Gwamnan ne ya bayyana haka yayin da ya ke kaddamar da kwamiti na musamman da zai kula da aikin ciyar da dalibai a makarantun sakandare 78 a fadin jihar.

A wurin kaddamarwar ne Kashim Shettima ya ce: “shirye-shirye na kan hanya inda za mu rika amfani da dalibai a matsayin ‘yan liken asiri wadanda ya ce za su rika tura masa sakon kar-ta-kwana ta wayar salula da soshiyal midiya, su na rika fada masa irin inganci da nagartar abincin da ake ba su, ta yadda duk ranar da aka dafa musu garau-garau, to zai iya sani.

Sai dai ba a sani ba ko gwamnan zai raba wa daliban wayoyin GSM ne da kuma sai musu data ta shiga soshiyal midiya.

Gwamnan ya yanke shawarar daukar matakin amfani da dalibai su yi masa liken asairi ne sakamakon wani samamen ziyarar bazata da ya taba kaiwa wata makarantar sakandire a cikin 2012, inda ya iske an dafa wa daliban abincin da kwata-kwata ba ya cikin jerin abincin da aka yarda a rika dafa wa daliban.

Share.

game da Author