Ba zan amsa tambayoyin kwamitin majalisa ba – Inji Idris Ibrahim

0

Sufeto janar din ‘yan sanda Ibrahim Idris ya ce bazai amsa tambayoyin da kwamitin majalisar dattawa ta yi masa ba saboda maganar na kotu.

Idris ya ce yin hakan saba wa dokar kasa ce da dokar majalisar dattawan.

Majalisar ta bukaci ya bayyana a gabanta domin yi mata bayani kan wasu zargi da akeyi masa wanda Sanata Misau ya zayyano su a zauren majalisar.

Sai dai kuma shugaban kwamitin Francis Alimikhena ya ce kotu ce take neman ta tsoma bakin ta a cikin aikin su domin majalisar ta kafa wannan kwamitin kafin a kai maganar kotu.

Ya ce batun da suke yin bincike akai daban da wanda ke kotu.

Kwamitin ta ce za ta buba bayanan da aka mika gabanta, sannan za ta sake gaiyatan Sufeto Janar din ‘yan sandan ya bayyana a gaban ta.

Share.

game da Author