An kashe ‘yan Boko Haram birjik, an ceto dan shekara 6

0

Askarawan Sojojin Nijeriya sun bayyana cewa sun kakkabe ‘yan Boko Haram a wani farmaki da sojojin su ka kai musu.

An kai wa Boko Haram harin ne a lokacin da su ka yi wata kumumuwa da nufin su kutsa cikin Dajin Sambisa a ranar Asabar.

Daraktan Hulda da Jama’a Burgediya Janar Sani Usman, ya bayyana haka a Maiduguri, inda har ya kara da cewa ‘yan ta’adda da dama sun tsere da mummunan raunuka a jikin su.

Ya ce Bataliya ta 151, su ne su ka yi wa Boko Haram din rubdugu tare da ceto wani yaro dan shekara 6 a lokacin da sojojin rundunar su ka yi wa ‘yan Boko Haram kwanton-bauna a kan hanyar Banki zuwa Bula, cikin Karamar Hukumar Bama ta Jihar Barno.

A ta bakin sa, an kama makamai da dama, da su ka hada da kekunan hawa takwas, addu’a da kuma tulin kakin Manyan Kwamandojin Boko Haram.

Share.

game da Author