Gwamnatin Tarayya ta bayyana wa Babbar Kotun Najeriya da ke Lagos cewa doka ya hana ta bayyana yadda aka kashe kudaden Paris Club har naira bilyan 388.
Wannan bayani ya fito ne daga Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, a matsayin raddi ga wata kara mai lambar FCH/CS/523/17 wadda kunyar nan ta bin diddigin yin aiki kan ka’ida ta SERAP ta shigar.
SERAP dai ta shigar da karar ce inda ta nemi kotu ta tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta bayyana yadda jihohi 35 su ka yi almubazzaranci da naira bilyan 388, kudin agaji da gwamnatin tarayya ta raba wa jihohi domin tsamo su daga halin kaka-ni-ka-yi.
Idan ba a manta ba, kwanan baya Shuhaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadin sa ganin yadda wasu jihohi ke kasa biyan albashi, duk kuwa da bilyoyin kudaden da aka rika narka musu, wadanda su ka wuce ka’idar adadin da ya kamata a bai wa kowace jiha.
Ofishin Babban Akawu na Tarayya ya shaida wa Mai Shari’a Hassan cewa kowace jiha na da cikakken iko kan kudaden shigar ta da kuma wanda ta ke kashewa.
Don haka ofishin sa ba shi da ikon tilasta jihohi su ba shi rahoton yadda su ka kashe kudaden su.