Masu iya magana dai sun ce ‘fara koyon mulki da baki, kafin ka fara koyo da hannu. Sai dai a bisa dukkan dalilai, wannan magana ba ta shiga kunnen mukarraban gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba, ganin yadda su ke yawan tubka da warwara a sha’anin tafiyar da gwamnati.
PREMIUM TIMES HAUSA ta yi nazarin irin shan-banten da makusantan Buhari ke yi. Amma ga muhimmai 11 da su ka gillara, wadanda bai dace a rufe ido, a bari su shude ba a yi nazarin su ba:
1. Mamayar da beraye su ka yi wa ofishin Shugaban Kasa ya sa shi kauracewa:
Gwamnatin Buhari ta sha suka da gwasalewa sakamakon sanarwar ta Fadar Shugaban Kasa ta bayar cewa beraye sun yi mummunar barna a ofishin Shugaban Kasa, har ta kai ba ya iya gudanar da aiki, ya kaurace, ya koma ya na tafiyar da mulkin kasar nan daga gida.
Hakan ta faru ne bayan dawowar sa daga London inda ya sha fama da jiyya. Masu lura da siyasar Nijeryu na nuna ra’ayin cewa an yi wa beraye kazafi ne kawai, ana so dai a bar Buhari ya kara murmurewa a gida kawai.
2. Ministoci ‘yan hayaniya ne kawai:
Yayin da abubuwa su ka fara rincabe wa Shugaba Buhari bayan ya dauki tsawon lokaci ba nada ministoci ba,
sai ya kare kan sa ta hanyar raina ayyukan ministoci, inda ya furka a wani taro da ya je kasar France, inda ya ce ministoci fa duk ‘yan hayaniya ne. Buhari ya kara da cewa ministoci surutai wakai su ke ba wani ayyukan a zo a gani ba.
Bai yiwuwa a ce gwamnatin Fedaraliyya za ta iya aiki ba tare da ministoci ba. Domin su da sauran ma’aikatan hukumar da take shugabanta kowa aikin da dokar kasa ta gindaya masa ya yi.
3. Beraye ne su ka gurgure takardun kasafin kudi:
Kuru-kuru Ministan Kiwon Lafiya na gwamnati Buhari, Isaac Adebiwole ya fito ya ce kasafin kudin Ma’aikatar sa ya samu matsala, domin beraye sun gurgure wasu haruffa, kalmomi da lissafin makudan kudade har da wasu sahihan bayanai da ke cikin kasafin.
Hakan ya zo daidai lokacin da ita ma majalisar tarayya ta ce beraye sun ci takardun kasafin kudin ta na 2016.
4. Gwamnatin PDP ce ta dawo da Maina:
Mukarraban Shugaba Buhari sun jefa shi, kuma sun jefa gwamnatin sa cikin kunya, daga baya kuma su ka shiga kame-kamen wanda za su dora wa laifin shigo da Abdulrashid Maina, tsohon shugaban hukumar fansho.
An yi da dabambadama tsakanin Ministan Harkokin Cikin Gida, Janar Dambazzau, Ministan Shari’a Malami da kuma Shugabar Ma’aikata, wadda a karshe ta ce da sanin Shugaba Buhari aka shigo da Maina kasar nan bayan gudun hijira da ya yi.
Bayanai daga iyalin Maina sun nuna Maina ya samu daurin gindi daga jami’an ‘yan sandan ciki, wato SSS aka dawo da Maina.
5. Matsin tattalin arziki ba gaskiya ba ce, tazuniya ce:
Haka Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosu ta taba rubutawa a shafin ta na Tweeter a baya cewa, surutan da ake yi na “Recession’, wato matsin halin rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya duk karya ce da kuma tatsuniya.
Yayin da aka yi mata caaa, sai Adeosu ta yi sauri ta cire wannan kalami daga shafin ta. Daga baya dai har murje idanu ta yi, ta ce shafin na Tweeter ba na ta ba ne.
Sai dai kuma kwana daya bayan wannan abin kunya, PREMIUM TIMES ta haska wani taro na fi a faifan bidiyo inda Kemi ta yi wannan kalami.
5. Laifin gwamnatin Jonathan wajen tsaikon Buhari dangane da nada ministoci
Mai yiwuwa Buhari ya manta a baya cewa ministoci ba su da wani amfani. Don haka kowace irin dadewa ya yi bai nada su ba, to ba abin damuwa ba ne.
Sai ga shi cikin Nuwamba, 2015 kuma ya ce rashin rantsar da bai wa sabbin ministoci ba na tsawon lokaci, duk laifin gwamnati Goodluck Jonathan ce.
Yayin da Buhari ya ce laifin Gwamnatin Jonathan ce saboda takardun bayanan mika mulki da ministocin Jonathan su ka rubuta, duk na bige ne ko gare.
Sai dai kuma a cikin jawabin na Shugaban Kasa, wanda Lai Mohammed ya karanta a madadin sa, babu inda ko da a wuri daya aka kawo hujjar wani wuri ko wasu wurare da Lai ya bada misali ko daya.
7. Buhari ya soke taron Majalisar Zartaswa domin ya karbi rahoton binciken Babachir da na tulin kudin Ikoyi:
Bayan dawowar Buhari daga jiya ranar 18 Ga Agusta, an shirya taron Majalisar Zartaswa a ranar 23 Ga Agusta, amma sai aka daga a bisa dalilin Buhari zai karbi rahoto daga Mataimakin sa Osibanjo, a gidan sa.
Jama’a sun yi mamaki sosai, ganin cewa ai karbar rahoto abu ne da bai wuce minti biyu ba. Kuma za a iya karba ko da a wurin taron ne.
Amma kuma abin mamaki, sai ga shi tun daga ranar 23 Ga Augusta, Buhari ya shafe watanni uku kafin ya kori wadanda ake zargin.
Idan ma za a iya tunawa, har wasika ya taba turawa a Majalisar Tarayya, inda ya tabbatar musu da cewa Babachir bai yi laifin komai ba. Daga baya sai Majalisar Dattijai ta ce ba ta yarda ba, sai dai a yi bincike.
8. PDP ce za a dora wa laifi a duk inda Gwamnatin Buhari ta kasa:
Cikin makon da ya gabata ne Shugaban Hukumar Kwastan Hamid Ali ya ce gwamnatin Buhari ta gaza a wasu bangarori, amma fa hakan na da nasaba da dimbin gyauron ‘yan PDP da ke cikin gwamnati wadanda su ke hana ruwa gudu a cikin gwamnati.
9. An soke taron Majalisar Dattawa saboda bukin Sallah:
Ranar Laraba, 6 Ga Satumba, an soke taron Majalisar Gudanarwa, a bisa dalilin cewa ministoci ba su shirya bayanan da za su gabatar ba, saboda sun shagaltu da hidimomi da bukukuwan Sallah. Haka Lai Mohammed ya furta a lokacin.
A lokacin dai sai 4 Ga Satumba za a yi Sallah, amma aka bayar da hutu tun ranar Juma’a 1 Ga Satumba da kuma Litinin 4 Ga Satumba, 2017. An yi Sallah Babba a ranar I Ga Satumba ne.
Wannan dalili dai ya jawo kace-nace a zukatan ‘yan Nijeriya masu bibiyar yadda gwamnatin Buhari ke aiki da kuma inda ta ke kwafsawa.
10. Yadda wani dan karafkiyar jami’in gwamnatin Buhari ya cusa batun banza a cikin jawabin da Shugaban Kasa ya karanta:
A baya dama har wasu kalamai da tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya yi, sai da aka taba kwasowa aka jibga a cikin bayanan Buhari.
Bayan da jaridar THISDAY ta fallasa wannan abin kunya, sai gwamnati ta ce wani dibgaggen mataimakin darakta ne a cikin Fadar Shugaban Kasa ya kwaso kalaman Obama, ya afka cikin na Buhari. A karshe dai Buhari ya ba ‘yan Nijeriya hakuri.
11. Kwakyariyar aringizo da kwange a wurin daukar sabbin ma’aikatan SSS.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES a cikin Afrilu, 2017 ta bankado yadda aka yi wa wasu jihohi azuraren adadin yawan wadanda aka dauka, yayin da wasu jihohin kuma aka yi musu kwange.
Wannan ma ya tayar da hayaniya a cikin kasa, har sai da ta kai an soke daukar a lokacin, aka ce a sake sabon lale.