Kwalejin Kimiya da fasaha na Kaduna ‘KADPOLY’ ta Janye yajin Aiki

0

Bayan share makonni 7 da sukayi suna yajin aiki malaman , Kwalejin Kimiyya da fasaha na Kaduna ta janye yajin aikin.

Da yake sanar da haka wa sauran ‘yan uwansa malamai, Abbas Muhammad ya ce sun amince da haka ne bayan zama ta musamman da kungiyar tayi.

Yayi kira ga sauran malam da su koma aji daga yau.

Idan ba a manta ba kungiyar ASUP a ranar 18 ga watan Yuli ta dakatar da yajin aikin da ta fara yi bayan ta tattauna da hukumar kwalejin kan biyan bukatun malaman sannna bada da watanni uku domin hakan su biya musu bukatun.

Ya ce bukatun nasu sun hada da;

1. Rashin biyan wasu alawus din malamai.

2. Rashin kayayyakin aiki na koyarwa ga dalibai.

3. karanci ofisoshi da kujerun zama.

4. Rashin gyara gine-ginen da ke kwalejin.

5. Karancin bandaki.

6. Rashin wuraren shakatawa da wasanni.

Share.

game da Author