Kundin tsarin mulkin APC na da tsari yadda za a fidda dan takaran shugaban kasa – Gwamnan Bauchi

1

Gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abubakar ya sanarwa manema labarai cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar su na APC ke da tsarin yadda za ta fidda dan takaran shugaban kasa idan lokacin haka yayi.

Abubakar ya fadi haka bayan taron jam’iyyar da akayi a hedikwatar ta dake Abuja.

Da aka tambaye shi game da abin da wani jigo a jam’iyya ya ce, Bisi Akande, wai Buhari bai sanar dasu ko zai yi takara a 2019 ba saboda haka ko waye jam’iyyar ta fitar zasu mara wa baya, Abubakar ya ce basu tattauna wannan Magana ba a zaman su.

Bayan haka kuma kwamitin zartaswan jam’iyyar ta amshi sakamakon wani aiki da gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai yayi game da ingancin tsarin mulkin da Najeriya ke bi a yanzu.

Share.

game da Author