Diezani ta nemi dawowa Najeriya, EFCC na neman hanawa

0

Hukumar EFCC ta garzaya Babbar Kotun Tarayya, a Abuja, domin rokon kada Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya bai wa tsohuwar Ministan Man Fetur a lokacin gwamnatin Goodluck Jonathan damar zuwa Nijeriya ta bayar da shaida a wata shari’a da ta shafe ta.

Dimgba, shi ne alkalin da ya umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ta ci gaba da shirin yi wa Sanata Dino Melaye kiranye.

Lauyan Diezani Allison-Maduekwe ne ya nemi alkalin ya rubuta wa Diezani sammacen kira, sannan ya aika ta hannun hukumar Ingila cewa ya na bukatar ganin ta a kotu domin ta masa tambayoyi a matsayin ta na mai shaida a wata shari’a da ke gaban sa.

Sai dai kuma lauyan EFCC, M.S Abubakar, ya rubuta wa kotun takarda mai kunshe da bayanai har shafi 18. Ya roki alkalin cewa bai kamata Diezani ta zo ba. domin can ma a London ana ta binckien ta ne dangane da kadarorin ta da aka rike, wadanda ake zargi duk na kudin sata ne daga gwamanatin Najeriya.

Abubakar ya ce Diezani na so ta yi ‘yar burum-burum ne, ta gudo daga London daga shari’ar da za ta fuskanta a can, sannan kuma idan ta zo nan ta yi iyar kokarin ta na ganin ta dagula dukkan binciken da EFCC ke mata.

Ya ce ya na son kotu ta tuna cewa, na farko dai Diezani guduwa ta yi tun cikin Mayu, 2014 zuwa Ingila.

Sannan kuma tawagar EFCC ta bi ta har London domin su yi mata tambayoyi, amma lauyoyin ta suka hana ta amsawa.

EFCC dai na so Ingila ta damka mata Diezani ne a hannun ta, a kamo ta daga can, ba wai wata kotu ta kira ta don ta zo Najeriya ta bayar da shaida a kotu ba.

Share.

game da Author