Iyalan Jonathan sun kara bayyana wasu kayan da ‘yan sanda su ka sace

0

Wasu bayanai sun kara fitowa daga hannun iyalan tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, inda su ka kira PREMIUM TIMES HAUSA, ta wayar tarho, su ka bayyana mata cewa sun karanta labarin da ta buga, sannan kuma su ka kara fallasa wasu kayayyakin da su ka ce ‘yan sanda sun sace a gidan, wanda ke lamba 89, kan titin Habiba Kalgo, wanda aka fi sani da Fourth Avenue, a Gwarimpa, Abuja.

Idan ba a manta ba, jiya Litinin ne mu ka kawo ma ku bincike na musamman inda ‘yan sandan da ke gadin gidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonatahan, su ka kwashe kayan gidan su ka saida wa ‘yan gwangwan arha bagas.

Majiyar, wadda ta ke da kusanci na kut-da-kut da Jonathan, ta bayyana cewa ‘yan sandan ba su bar komai a gidan ba, saboda hatta kofofin dakuna da falo-falon gidan duk sai da su ka gaggabe su, su ka sayar.

Sun kuma sayar da kayan kicin na gidan tare kuma da manyan ma’ajiyar suturu, wato wardrobe na gidan kakaf. Majiyar ta kara furta wa Premium Times Hausa cewa hatta kwandon tsuguno a yi bayan gida duk sun gaggabe su, sun sayar.

“Mu a halin yanzu babu wani hanzari da za mu iya yi, domin ‘yan sandan da aka ba aikin gadin gidan mu ne su ka yi masa kankat, su ka saida kayan. Har talbijin da sauran kayan wutar gidan sun ciccire, sun sayar.”

Wani bincike da Premium Times Hausa ta kara yi, ya tabbatar da cewa hatta kyawaren tagogin gidan duk an ci kasuwar /yan gwangwan da su.

Sai dai kuma a jiya ne rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, ta yi borin-kunya, inda awa biyu kacal bayan PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin satar da aka dibga wa Jonathan, sai kakakin ‘yan sandan, Mamza Anjuguri, ya fitar da takarda ga manema labarai ya sanar da su cewa ana tsare da wasu ‘yan sanda a bisa zargin salwantar wasu kaya a gidan Jonathan. Sun kuma yi alkawarin cewa za su sanar da sakamakon binciken da su ke yi.

Idan ba a manta ba, a rahoton PREMIUM TIMES na jiya Litinin, an bayyana yadda aka yi ta kulli-kurciya da Anjuguri har tsawon kwanaki hudu domin ya tabbatar da batun satar da kuma kame ‘yan sandan, amma ya na cewa a ba shi lokaci ya yi bincike.

Share.

game da Author