APC: Idan ba a duba rikicin Kaduna ba za a iya fadawa cikin tsaka mai wuya – Shehu Sani da Sule Hunkuyi

0

Sanatocin da ke waliltan Kaduna ta Tsakiya da ta Arewa sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi sun kai kukan su hedikwatar jam’iyyar APC kan zargin da suke yi wa wasu ya’yan jam’iyyar da yin babakere da murkushe duk wani dan jam’iyyar da ba ra’ayinsu daya ba.

Bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban jamiyyar John Oyegun Sanata Shehu Sani da yake ganawa da manema labarai ya ce idan ba a yi hankali ba jam’iyyar APC za ta iya faduwa matsalar da PDP ta shiga a 2015.

” Zaben da akayi na delight a Kaduna ba zabe bane domin wasu ne kawai suka zauna a zaurukansu suka nada wanda zasu nada amma samsam ba a yi zabe a Kaduna ba.

” Saboda haka muna kira ga Uwar jam’iyyar da ta duba wannan kuka na mu ta bi mana hakkin mu a matsayin mu na ya’yan jam’iyyar a jihar.”

Share.

game da Author