Gwamnain Tarayya ta bayyana cewa ta dogara kacokan a kan Dangote da ya kokarta kammala ginin matatar danyen man fetur, domin ta cika alkawarin da ta daukar wa ‘yan Najeriya cewa nan da 2019 za a daina shigo da man fetur daga kasashen waje.
Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Ibe Kachikwu, wanda ya kai ziyara a masana’antar tace danyen man fetur da Dangote ke ginawa a Lekki, Lagos, ya ce gwamnati a shirye ta ke a na ta bangaren domin ta taimaka wajen ganin cewa an kammala aikin ginin matatar kafin wa’adin da aka dauka za a kammala aikin.
Ministan, wanda ya ce ya gamsu kuma ya yi mamakin irin yawan gagarimin aikin da Dangote ya kinkimo, ya ce wannan gwamnati mai ci yanzu ta na da yakinin cewa ‘yan kasuwa ne kashin bayan gina masana’antun da gwamnati ke son ingantawa a kasar nan. Don haka a cewar sa, ga babban misali nan ana gani a irin ayyukan da Dangote ke gudanarwa.
Da ya ke maida magana, Shugaban Rukunonin Masana’antun Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ya karbi wannan kalubale da minista Kachikwu ya ba shi, don haka da yardar Allah zai kammala aikin ginin masana’antar kafin 2019.
Abin da minista ke kokarin yi, shi ne abu mafifici ga kasar nan. Mu dama matsalar mu a nan Afrika ita ce sai dai mu sayar da kaya zallan su a waje, ba mu sarrafa su kafin mu fitar.
“Don haka, kamar minista na cewa ne mu yi abin mu a nan da kan mu. To ina fata ko da Nijeriya ta na hako gangar danyen mai milyan 2.5 a kowace rana, to za ba mu rika fita da mai kasashen waje ana tacewa ba.” Cewar Dangote.