EL-CLASICO: Yadda ragamar kwallon duniya ta subuce daga hannun Barcelona

0

A yau PREMIUM TIMES HAUSA na dauke da Nazari Na Musamman dangane da yadda harkar kwallon kafa ta juya wa Barcelona baya, tun bayan da Zinedine Zidane ya zama mai horas da ‘yan wasan Kungiyar Real Madrid. Za ku ji dalilan faruwar hakan.

Wane irin daci ne Madrid ta dandana cikin shekaru bakwai a hannun Barcelona a baya? Ko Madrid za ta dade ta na jan zaren ta a duniya, ko kuwa tashin-gishirin Andurus za ta yi, daga bana shikenan?

TAKUN SABON SALON WASAN KWALLO

Hankalin masu shawa’ar kallo da kuma nazarin kwallon kafa ya karkata daga kasashen Italy da Ingila ne, tun bayan da tauraron Diego Maradona ya dusashe, bayan kammala gasar cin kofin duniya na shekarar 1994, da aka gudanar a birnin Atalanta, Jihar Georgia a Amurka. Tsakanin wannan shekara zuwa 1999, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da takawarar ta, ta Arsenal sun yi sharafi a Ingila, inda fitatun ‘yan wasa irin su David Beckham, Terry Henry da Christiano Ronaldo da wasu da dama su ka rika cin Karen su babu babbaka.

KARKATAR AKALAR KWALLO ZUWA SPAIN

Hijirar da Zidane ya yi daga Juventus zuwa Real Madrid da kuma wacce David Beckham ya yi daga Manchester United shi ma zuwa Real Madrid, ta fara karkatar da hankulan masu kallo da sha’awar kwallon kafa zuwa kasar Spain, inda a lokacin kingiyar Barcelona ta yi wani dogon yunkuri, har ta na gogayya da Real Madrid a lokacin.

Kaka-gidan da Zidane, Beckham, Ronaldo na Brazil da kuma Lious Figo su ka yi a Real Madrid, tare da hadewar su da tauraron Spain, Raul Gonzalez, ya haifar da samun wani gungun ‘yan wasa mashahurai a Real Madrid, wadanda a duniya aka rika kira da suna Glacticos, watau Taurarin Duniya.

Yayin da su ka fara yin gwagwagwa da Barcelona, ita kuma kungiyar ta Barcelona ta sai ta yi gamo-da-katarin nasarar kyankyashe ‘yantsakin da ta ke kiwo a karamin kulob din ta, watau Team B, irin su Andrea Iniasta, Xabi, Messi da sauran su, su ka zama taurarin da ake ji da su a babban kulob din.

Barcelona ta ga cewa ko ka na da kyau, to ka kara da wanka. Dalili kenan su ka yi tashin – gwauron – zabo, su ka sayo Roanaldinho. Zuwan Ronaldinho ya kara daukaka Barcelona, musamman hadewar sa da Messi, Xavi, Iniasta da kuma David Villa, wanda aka saya daga Valencia.

Tun daga nan sai harkar kwallo ta koma a duniyar kwallon Spain, kungiyar Barcelona ta hadu, kamar yadda ita ma Madrid ta hadu. Sai dai kuma ‘yan kishi da ‘yan ra’ayin rikau a Spain, sun fi nuna kauna ga Barcelona, ganin yadda ita a lokacin ta fi maida kai ne wajen kyankyashe yara ‘yan kasar, sabanin Madrid, wadda ta fi karkata wajen fitar da tsabar kudi ta na sayen ‘yan wasa haifaffun wasu kasashe.

ADAWAR BARCELONA DA REAL MADRID

Tsananin gaba ya shiga tsakanin Barcelona da Real Madrid, tun bayan hijirar da Figo ya yi zuwa Madrid.

Sai kuma ya kasance takun wasan Barcelona ya sha bamban da na sauran kungiyoyin kwallo na duniya, inda su, su ka fi bayar da karfi wajen kwarewa kan iya ba-ni-in-ba-ka ta kurkusa. Yayin da su kuma Madrid, gogaggu ne wajen iya zari-ruga da kuma cilla wa dan wasa kwallo ya tare a duk iyar nisan sa, sai kuma maida hari kan abokan adawa da hanzari, wato counter attack.

Kwarewar takun wasan kungiyoyin biyu ya sa masana kwallo, masu sharhi da manyan ‘yan jaridu na duniya su ka sa wa kowace haduwa za su yi, sunan wasan El-clasico, watau, wasan gwanaye ko taurarin da duniya ke ji da su.

An sha yin kare-jini, biri-jini a baya, idan kungiyoyin biyu sun hadu. Zuwan mai horas da wasa Pep Gordiola, wanda tsohon dan wasan Barcelona ne ya sa Barcelona ta rika kwance wa Real Madrid zani a kasuwa, har ma a tsakar gidan ta Barcelona ta sha sabule mata wando, inda ta rika rama duk wani cakarkaca da Madrid ta rika yi mata a baya can zamanin su Kluivart ko Samuel Eto’o.

KAKA-GIDAN MESSI DA RONALDO A DUNIYA

Duk wani mai shawa’awar kallon kwallo a duniya ya na sha’awar kallon karawar kungiyoyin biyu, musamman ganin yadda ‘yan wasa biyu na bangarorin biyu ke barje-gumen su wajen yi wa bangarorin juna mummunar barna. Wadannan ‘yan wasa kuwa su ne Leonel Messi da kuma Cristiano Ronaldo.

Su biyun sun jima su na tsone wa sauran ‘yan wasan duniya idanu, ta hanyar hana zakarun ‘yan wasan yin wata cara a duniya, sai dai su biyu kawai. Duk wani gwarzon wata bajinta a Turai ko a duniya, idan ba Messi ba ne, to Ronaldo ne. Ko a samun kudin su ta hanyar albashi da sauran tallace-tallacen kamfanoni, za a iya cewa a Nijeriya tun daga kansila har shugaban kasa, babu wanda albashin sa na wata shida ya kai yawan kudin da Ronaldo ko Messi ke samu a kowane sati – ko sun buga kwallo, ko ba su buga ba.

Real Madrid sun samu mummunan targade daga a farkon shekaru goma da su ka gabata, ta inda su ka rika canja masu koyar da wasa, tamkar yadda mai wadatar sutura ke yawan cire riga ya sauya wata, idan ta yi datti. Zuwan Jose Mourinho daga Inter Milan ta Italiya zuwa Madrid, ya samar wa magoya bayan kungiyar bakin magana. Haka ma kawo dattijo Carlo Anceloti a matsayin mai horas wa da kungiyar ta yi.

ZIDANE DA JUYIN ZAMANI A REAL MADRID

Kama aikin da Zidane ya yi daga mai horas da karamar kungiyar Real Madrid zuwa babbar kungiyar, ya haifar da wani juyin zamani ga Real Mardid, ta yadda daga watan Janairu, 2016 zuwa yau, watanni 20 kenan, ya kafa tarihi har guda 18 a kungiyar, wadanda kafin zuwan sa, kungiyar ba ta taba kafa tarihin a baya ba.

Dama kuma Zidane tsohon dan wasan Madrid ne, kuma shi ne mataimakin Carlo Ancelotti a kakar wasan 2013/2014, bayan an yi nasarar lashe kofin Champions League ne aka maida shi ya na koya wa karamin kulob din Madrid, wanda dan sa Enzo ke ciki a lokacin.

Kadan daga cikin wasu nasarorin da Zidane Real Madrid ta samu a karkashin Zidane, su ne, a karkashin sa, Madrid ta yi wasanni 68 a jere ba ta taba fashin jefa kwallo a ragar abokan karawar ta ba. A zamanin sa ne kuma kungiyar ta taba jera wasanni mafi yawa ba tare da an yi nasara a kan ta ba.

Har ila yau, a cikin watannin nan 20, Real Madrid ta ci manyan kofuna har guda 7, inda na baya-bayan nan shi ne kofin Gwanayen Spain wanda ta lashe a hannun Barcelona, a ranar Laraba, bayan ta yi nasara a kan ta da kwallaye 5-1 a wasanni biyu.

MATSALOLIN BARCELONA

Alamomin matsaloli tattare da Barcelona sun fara fitowa ne tun bayan karbar ragamar jagoranci da Zidane ya yi wa Real Madrid, a Janairu, 2016. A lokacin da ya karbi ragamar, an rigaya an ci rabin Kakar Wasannin 2015/2016, kuma akwai ratar maki 15 tsakanin kungiyar da Barcelona wadda a rukunin su ita ce a sama. Amma a karshe da kyar da gumin goshi Barcelona ta yi wa Madrid ratar maki daya tal ta lashe kofin La Liga na shekarar.

Kofuna 7 da Madrid ta lashe a cikin watanni 20 kacal, ya babbatar da cewa daben ta ya ji makuba sosai. Ta samu wadannan nasarori ne a daidai lokacin da gwanayen ‘yan wasan Barcelona irin su Xavi, David Villa sun bar kungiyar saboda shekarun su sun ja sosai. Yayin da Puyol ya yi ritaya daga kwallo.

Ritayar Puyol da sakacin Barcelona na sayar da Dani Alavis ga Juventus, ya haifar da baraka ga bayan Barcelona, ta yadda Gerrad Pique a yanzu ya ke saurin gajiya ko kuma yawan jefa kwallo a ragar su.

Andrea Gomes da Umtiti duk za a iya cewa har yau kwalliyar su ba ta biya kudin sabulu a Barcelona ba.

SAKACIN BARCELONA A KAKAR SAYEN ‘YAN WASAN BANA

Duk da cewa Barcelona ta rabu da manyan ‘yan wasan ta da dama, kuma ba su da kwararru ‘yan ko-ta-kwana da ke kan benci, hakan bai sa ta kwashi kudi ta sayi fitattun ‘yan wasa a kasuwar cefanen ‘yan wasa na ba ta ba.

Maimakon haka, sai ta yi wani sakacin barin Neymar ya canja sheka zuwa PSG ta kasar Faransa. An yi zaton Barcelona za ta yi amfani da tsabar kudin da ta sayar da Neymar wajen sayen ‘yan wasan da za su yi gogayya da Madrid, amma sai kungiyar ta buge ga neman mai share mata hawaye a kasar China, wato Paulinho.

ALAMOMIN KARKON REAL MADRID

Tafiyar fitattun ‘yan wasa irin su Moratta, James Rodriguez, Pepe, Jese da Danilo daga Madrid, bai gurgunta kungiyar ba, sai ma karfin da ta kara samu ta hanyar rike Isco Alarcon, dan lelen kungiyar a yanzu, da kuma sabbin jini da suka taso irin su Assencio, Ceballos, Theo Hanandez da ta sayo dukkan su a arha bagas, kuma dukkan su ko a wasan da su ka kafsa da Barcelona a wannan satin, sun nuna wa duniya cewa sun zama na-kawo-karfi wanda Hausawa su ka ce, ya fi wane-ya-girme-ni.

Kada a manta, duk da cewa Moratta ya bar Madrid, har yanzu ruwan Karim Benzama na maganin dauda. Barcelona ta shaida haka a wasan karshe na cin kofin da aka buga a daren Laraba. Ga shi kuma ana tunanin cewa Madrid na tsimin Borja Mayoral da yaro sabon jinin da ta yi wa cinikin-biri-a-sama, watau Vinicious Jr., wanda ke buga wasa a kungiyar Flamingos ta Brazil, da aka rattaba hannun sai karshen kakar wasan 2018 zai koma Madrid.

Wadannan ‘yan wasa su ne Madrid za ta kara jan zaren ta da irin su tsoffin ‘yan wasa kamar Ronaldo, Marcello, Ramos, Benzama da Modrics tare da su, kafin su zama masu maye gurabun su.

A wannan lokacin kuwa, zai iya kasancewa Barcelona ba ta gama sheshshekar gudun kai gwauro da kai marin neman ‘yan wasan da za su fidda ta kunya a ranar jin kunya ba.

INA MAFITA?

Fitaccen dan wasan Barcelona Gerrard Pique, ya bayyana a daren Laraba cewa: “Tun da na ke wasa sheakara 9 a Barcelona, ban taba jin Real Madrid ta kaskantar da ni ba kamar wannan satin, inda ta yi mana dukan-kabarin-kishiya.”

Masu nazarin harkokin kwallo na yin tsinkayen cewa ya kamata Barcelona ta farka daga barci, domin ta sake hawa turbar yin gogayya da Real Madrid, wanda hakan shi ne zai kara wa wasa da siyasar kwallon kafa armashi a duniya.

Yayin da ‘yar manuniya ta nuna matsalar Barcelona, da yawa na cewa a halin yanzu Messi ne kadai kwarjinin kungiyar.

Idan aka cire shi, wasu na ganin cewa Barcelona ba ta da wani bambanci da Aston Villa. Hakan kuwa babban cikas ne a duniyar kwallo, wanda su kan su magoya bayan Madrid ba za su so a ce toron giwar su ba shi da abokin karon-battar fadan gwangwa-da-gwangwa ba.

“Duk yadda ka zama gwarzo, idan ba ka da gwarzon da zai iya tunkarar ka kan sa tsaye, to ta ina za ka iya gwada karfin ka?’’ Inji wani Balarabe a shafin sa na ‘tweeter’ yayin da yak e nuna bacin ran sa kan matsalar Barcelona.

Wannan batu na sa kusan haka ne, domin a wasan da Madrid ta yi nasara a kan Barcelona da ci 2-0, shahararru irin su Ronaldo, Isco, Gareth Bale duk ba su buga ba. Casemero ma sai a kusan karshe ya shiga. A hakan ma, da yawan magoya bayan Barcelona kagara su ka yi a tashi, don kada labari ya kara shan-bamban.

Share.

game da Author