A kawo karshen rikicin hukumar inshorar lafiya ta kasa – Kungiya Likitoci

0

Kungiyar likitoci ta kasa ‘Guild of Medical Directors GMD’ ta yi kira ga gwamanti da ta hanzarta sassanta rikicin dake tsakanin hukumar inshorar lafiya ta kasa da ma’aikatan kiwon lafiya da yaki ci yaki cinyewa.

Kungiyar ta ce matsalolin da hukumar inshorar lafiya ke fama da su ya hana ma’aikatan biyan bukatun mutanen da suke cikin shirin inshorar.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa. Usman Yusuf kan zargin wawushe wasu kudaden hukumar.

Ministan bayan hakan ya maya gurbin Usman Yusuf da Attahiru Ibrahim a hukumar har sai bayan an kammala gudanar da binciken da akeyi.

Shugaban kungiyar Femi Dokun-Babalola ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi wa asibitoci masu zaman kansu rajista cikin wannan shiri na inshorar lafiya domin yin hakan zai taimaka wajen samar da kiwon lafiya wa mutane a asibitoci da ke kusa da su.

Share.

game da Author