A ranar Alhamis ne shugaban kula da kiyaye yaduwar cutar kanjamau na kasa Sani Aliyu ya zayyana wasu dalilan da ke sa ana samun cikas wajen samun nasara a inshorar kiwon lafiya Najeriya.
Ya bada wannan bayanai ne a taron hadin guiwar da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta shirya a Abuja kamar haka;
1. Rashin samar da inshorar lafiya wa talakawan kasa wanda dama itace dalilan kafa hukumar tun farko.
2. Inshoran ta yi rijistan ma’aikatan gwamnati ne kawai sannan kashi 1.5 cikinsu ne ke amfana da shirin.
3. Gwamnati bata samar da isassun kudade wa fannin kiwon lafiya ba.
4. Rashin kishin kasa da tattali da mafi yawan mutanen Najeriya ke da shi da ya sa wadanda hakkin kula da shirin gwamnati ke hannun su ke wawushe kudaden da aka samar.
Bayan hakan ya bada wasu shawarwarin na hanyoyin da gwamnati za ta iya bi don shawo kan irin wadanna matsalar.
Ya ce gwamnatin za ta iya kara yawan kudin haraji musamman akan kayayyakin da suke kawo illa ga kiwon lafiyar mutane kamar sigar, kayayyakin zaki da sauransu. Hakan zai sa asami karin kudaden shiga.
Ya ce kamata ya yi a samar wa talakawan kasan damar shiga cikin wannan inshoran.
Daga karshe ya ce gwamnati ta tsara wata shiri da zai dunga bada bayanan akan yadda ma’aikatan ta suka kashe kudaden da take samarwa a fanin kiwon lafiya.