Gwamnatin tarayya ta rage tsawon lokacin da masu fama da cutar tarin fukan da ake ba magani na musamman da da yakan kai watanni 20 zuwa watanni 9.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da haka ranar Litini a lokacin da yake kaddamar da wani sashe inda mutanen da ke fama da cutar tarin fukan da baya jin magani za su iya karban magani a babbar asibitin gwamnatin dake Ibadan jihar Oyo.
Isaac Adewole ya yi kira ga duk wadanda suke dauke da cutar da su hanzarta zuwa asibitin gwamnati mafi kusa da su domin samun kulan da ya kamata.
Ministan ya ce ana iya warkewa daga cutar idan har dai an fara karban magani da wuri sannan kuma hakan zai taimaka wajen karfafa guiwar wadanda suke dauke da cutar fitowa domin samun magani.