Mai Magana da yuwan kamfanin ‘Dangote Group’ Tony Chiejina ya karyata zargin da ake yi wa shugaban kafanin Aliko Dangote cewa wai ya ba tsohon kakakin majalisar jihar Kano Kabiru Rurum toshiyar baki na naira miliyan 100 domin majalisar ta dakatar da ci gaba da binciken sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
Dalilin haka ya sa shi kansa kakakin majalisar ya yi murabus ganin cewa an yi masa ca kan da wannan zargi.
Tony Chiejina ya shawarci kwamitin da majalisar dokokin ta kafa ta gudanar da bincike akan wannan zargin da su yi kunnen uwar shegu da hakan domin bata lokacinsu za su yi kawai.
Gidan jaridar Daily Nigeriya.com ta ruwaito cewa Dangote ya bada kudin da ya kai Naira miliyan 100 wa tsohon kakakin majalisar jihar domin a dakatar da binciken da ake yi a wancan lokacin wanda Rurum ya musanta wanna Zargi.
Tsohon Kakakin majalisar jihar, Rurum ya ce anyi masa wannan kazafi ne don a sanya rashin jituwa a majalisar sannan kuma a ci mutuncin Dangote.
“Wannan kazafin duk karya ne domin ban taba hira da Dangote ba akan komai a ballantana ace wai har ya bani cin hanci.”
“Dama bisa ga yanayin mulkin dole ne gwamnan jihar ya neme mu akan haka.”
“Saboda hakan gwamnan jihar Kano ya aika da wasikarsa yana rokan alfarman mu da mu dakatar da wannan bincike da muke yi saboda zaman lafiyar mutanen jihar.”