Mutane sun rage kamuwa da cutar Kanjamau a Najeriya

0

Shugaban hukumar kula da hana yaduwar cutar kanjamau na kasa NACA Sani Aliyu ya ce an sami nasarar rage yadda cutar Kanjamau ke yaduwa a Najeriya.

Ya ce as sami raguwa sosai na mutanen da ke kamuwa da cutar.

Sani Aliyu ya ce an sami nasarar haka ne saboda yawa-yawan tallafin da suke samu daga kungiyoyin bada tallafi na kasashen waje sannan ya yi kira ga gwamnati da ta mai da hankali wajen kara samar da kula ga masu dauke da cutar kafin irin wadannan tallafi su dai na zuwa.

Ya ce gwamnatin samar da kulawa ga mutane 60,000 cikin miliyan daya da ke dauke da cutar kanjamau ta shirinta na ‘Taraba da Abia Projects’. Su kuma mutanen 940,000 na samun kulawa ne daga kudaden tallafin da Najeriya ke samu daga kasar Amurka da asusun bada tallafin na duniya.

Daga karshe Sani ya ce za suyi kokarin ganin an kara yawan mutanen da ke samun magani da kaso mai yawa cikin masu dauke da cutar.

Share.

game da Author