Ba zan yi biyyaya ga dakatar da ni da Ministan Kiwon Lafiya ya yi ba – Farfesa Usman Yusuf

0

Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta kasa Dr. Usman Yusuf ya ce ba zai yi biyayya ga dakatar dashi da ministan kiwon lafiya, Farfesa Isaac Adewola yayi ba saboda yin hakan da yayi ya saba dokar hukumar.

Dr Usman Yusuf ya ce dokar hukumar bai ba ministan ikon iya nada shi ba, korar sa ko dakatar dashi ba saboda haka yan nan a matsayinsa na shugaban hukumar Inshorar lafiya ta kasa.

Bayan haka Yusuf ya ce har yanzu bai ga wani abu da yayi na laifi ba da ministan ke ta bibiyarsa. Ya ce idan har maganar wai don hukumar ICPC na tuhumar sa ne to ashe da jami’an gwamnati da yawa sun na daure yanzu ko kuma sun ajiye aiyukansu domin akwai ire-iren wadannan kararraki a ICPC da ya kai sama da 180 a gabanta da ya hada da wasu ministoci.

Ya ce shugaban kasa ne yake da ikon nada shi ko ya dakatar dashi amma ikon da ministan yak e dashi bai kai ga ya dakatar dashi ba.

Share.

game da Author