Tun bayan nada shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa Dr Usman Yusuf aka fara takun tsaka tsakaninsa da ministan kiwon lafiya Isaac Adewole.
Wasu daga cikin dalilan da ma su fashin baki kan al’amuran yau da kullum suka bankado ya hada da nuna isa ce da mulki kawai amma ba wai don akwai matsala ba ko kuma akwai tabbacin barnata kudin gwamnati da akayi a hukumar NHIS din.
Shi dai Dr Usman Yusuf farfesa ne kuma kwararren likita mazaunin kasar Amurka. Bayan samun nasarar jam’iyyar APC a zaben 2015 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi shi da ya dawo saboda kwarewarsa ya rike hukumar Inshorar Lafiya ta kasa.
Dalilin yin hakan kuwa shine domin ya yi amfani da kwarewarsa a harkar kiwon lafiya don bunkasa shirn NHIS din da kuma samar wa talakawar kasar nan inshorar lafiyar.
Yanzu zaka ga talaka tukuf a wasu daga cikin manya manyan asibitocin kasarnan ya na goga kafada da masu hali a asibiti. Da ka tambayi yadda ya samu wannan damar sai ya ce maka NHIS ne.
A bayanai da minista Adewole ya yi kan dalilan da ya sa ya dakatar da Dr Yusuf daga hukumar NHIS sun hada da wai don a sami damar gudanar da binciken da ya kamata kan zargin da ake masa na yin amfani da kudaden da ya kai naira milliyan 200 wajen tura wasu daga cikin ma’aikatan hukumar karo ilimi wato (Training).
Minista Adewolwe ya ce ya na so ayi bincike kan haka ne ba tare da shi Dr Yusuf din ya na kan wannan kujera ba.
Shi ko Dr Yusuf ya ce ba zai bi umarnin ministan ba domin bashi da hurumin dakatar da shi a dokar ma’aikatar.
Wasu masu sharhi sun danganta wannan matsala da Yusuf ke fuskanta da rashin shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Shi minista ya na amfani da hakan da karfi da kusantar sa da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo domin muzguna wa Dr Yusuf domin baya samin yadda yake so da ga hukumar.
Masu yin nazari sunce sau dayawa ministan yakan aika da bukatunsa hukumar amma Dr Yusuf zai ce ba haka ba.
A wani rahoto da ba a tabbatar da ingancin ta ba ance ministan ya taba aikawa hukumar NHIS ya na neman ta bashi miliyoyin kudi da bukatar ta siya masa motoci wanda shi Dr Yusuf bai yi hakan ba.
Dr Yusuf ya zargi ministan da shirya masa Tuggu domin ganin an tsige shi daga hukumar.
Ya ce maganar kai shi hukuma ICPC abu ne wanda akeyi wa jami’an gwamnati kuma idan wai hakan ne zai zama dalilin dakatar dashi ashe da sama da manyan ma’aikatan gwamnati 180 da wasu ministoci ba sa aiki yanzu.
Yanzu dai kowa ya wasa wukarsa, minista ya ce ya dakatar da Dr Yusuf na nan daram dam, shi kuma Dr Yusuf ya ce minista bashi da hurumin dakatar dashi daga hukumar a doka.