Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki a ofishinta da ke Abuja.
Ana zargin Saminu Turaki da wawushe kudaden jihar Jigawa a lokacin da yake gwamnan jihar Jigawa.
Hukumar ta ce ba za ta saki Saminu ba har sai ranar da za ayi zama na gaba a kotu domin ci gaba da sauraren karan.