Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta fitar da jadawalin ranakun yi wa Sanata Dino Melaye kiranye. Hukumar ta fitar da jadawalin ne ranar Linitin a kan Sanatan mai wakiltar Kogi ta Yamma.
Wannan yinkuri da hukumar zaben ta yi, ya zo daidai ne da lokacin da lauyoyin Melaye ke ta kokarin neman kotu ta hana hukumar fara yin wannan matakan domin yi masa kiranye.
Dama tun cikin makon da ya gabata ne INEC ta tabbatar da cewa ta amshi kwafen koke da korafi daga ‘yan mzabar Melaye masu son su dawo da Melaye a bisa cewa bay a yi musu wakilci nagari a majalisar dattawa. Kwafen korafinnya nuna cewa kashi 52 na ‘yan mazabar Dino sun rattaba hannun yi masa kiranye.
Tuni dai Melaye ya garzaya kotu a hannun lauya Mike Ozekhome, inda ya ke rokon Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakatar da hukumar zabe daga fara shirye-shiryen aza ranar da za a fara yi masa kiranye.
Ita kuwa hukumar zaben tuni ta rubuta wa Melaye wasika cewa a ranar 3 Ga Yuli ne za ta fara sa-ido kan matakan yi masa kiranye.
Dino Melaye ya firgita, bayan INEC ta sa ranakun yi wa Sanatan kiranye
Dangane da wannan rikita-rikitar da ke neman rikitowa kan Dino Melaye, INEC ta bayayyana cewa don kawai an kai lauyan Dino ya garzaya kotu, hakan bai isa hana hukumar ci gaba da aikin tantance sa hannun yi wa sanatan kiranye da za a fara gudanarwa ba.
Sai dai kuma kallo na neman komawa sama, domin a zaman da Majalisar Dattawa ta yi a yau Talata, Sanata Melaye ya roki majalisar da ta rufa masa asiri ta sa baki, kada ta bari a yi masa kiranre. Ya ce gwamnan jihar Kogi ne ya hada duk wani tuggun neman a yi masa kiranye ya koma kauye, daga majalisa.
Da ya ke jawabi, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ikweramadu, ya bayyana cewa ba za su bari a watsa wa Melaye kasa a ido ba. Za su yi bakin kokarin ganin sun hana a tsige shi daga kujerar sa ta hanyar yi masa kiranyen da ake shirin yi.
Ikweramadu ya ce majalisar dattawa za ta tantance sunayen wadanda suka sa hannu domin neman yi wa Melaye kiranye.
Sai dai kuma masu lura da al’amurran siyasa sun nuna cewa babu ruwan majalisa da batun tantance sunaye, aikin hukumar zabe ne, ba na majalisa ba, don haka ne ma dokar kasa ta bai wa INEC ikon yin tantancewar, amma ba ta bai wa majalisar dattawa ba.
Ranakun fara tantance kuri’un kiranyen Sanata Melaye
1. 10 Ga Yuli, 2017: Za a manna wannan sanarwa a ofishin INEC na Karamar Hukumar Lokoja
2. 30 Ga Yuli, 2017: Ranar rufe karbar sunayen kungiyoyin da ke sha’awar zuwa domin sa-ido yayin kiranye. A hedikwatar hukumar zabe ta kasa ne za a karbi sunayen kungiyoyin.
3. 10 Ga Agusta, 2017: Ranar rufe karbar sunayen ajen na aikin tantancewar neman yi wa sanatan kiranye.
4. 15 Ga Agusta, 2017: Taron masu ruwa da tsaki a ofishin INEC na Jihar Kogi.
5. 19 Ga Agusta, 2017: Aikin tantancewa da za gudanar a kowace rufar zabe na mazabun Dino Melaye.
6. 19 Ga Agusta, 2017: Bayyana sakamakon tantancewar da aka yi a ofishin INEC na karamar hukumar Lokoja.
Discussion about this post