Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma ya roki Sanatoci da su saka baki kan kokarin da mutanen mazabarsa ke yi na yi masa kiranye.
Da ake tattauna batun yau a zauren majalisar, Sanata Dino ya roki yan uwansa da su taimaka masa wajen ganin shirin da yake zargin gwamnan jihar Yahaya Bello ya shirya masa don ganin anyi masa kiranye daga majalisar bai samu nasara ba.
Mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ekweremadu wanda shine ya jagoranci zaman majalisar ya yi wa sanata Dino alkawarin cewa majalisar za ta mara masa baya, cewa ya dauka wannan magana kamar ba ayi shi bane.