Tirka-tirkar amfani da mitar lantarki: Mazauna garin Kano sun koka da rashin dadewar wuta idan suka yi lodi

0

Game-garin talakawa da su ka fata amfani da tsarin amfani da wutar lantarki ta hanyar mita a Kano, sun bayyana cewa su na shan lantarki da dan karen tsada.

Bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar a Kano, a lokacin shagulgulan Sallah karama, ya tabbatar da haka, ta hanyar tattaunawa da jama’a da dama, a unguwannin da dama. A Kano dai tuni aka fara raba wa jama’a mota kyauta a karkashin kamfanin raba wutar lantarki na KEDCO.

Malam Nazir Mohammed mazaunin Karkasara, ya shaida wa PREMIUM TIMES Hausa cewa ba ya nan ya tafi neman abinci a cikin azumi, sai kawai ya dawo gida ya ga an makala masa mita a kofar gida.

“Da ya ke mu uku ne ke haya a gidan, mun had a naira 4,500 mu ka sayi yunit na wuta, tamkar dai yadda ake sayen katin wayar salula. To inda tsiyar ta ke, na naira 4,500 din nan ba zai yi maka sati biyu ba.”

Nazir ya ci gaba da cewa kafin fara amfani da mota kuwa, su na biyan naira 3,000 a duk wata. Ya ce to ka ga idan kuwa haka ne, batun alkawarin inganta mana wutar lantarki da aka yi alkawari a lokacin zabe, ya zama soki-burutsu kenan.

Duk da cewa ana samun wuta sosai a yanzu a unguwanni da dama, hakan bai burge Musa Tanimu mazaunin Kabuga ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta yi tattaki a yankin inda ta gano cewa unguwar na daya daga cikin shiyyoyin da KEDCO ta fara raba mita kyauta a Kano.

“An zo an kafa mana mota kyauta, mu na shan wuta, amma wannan tsada ai shan-wutar-tsire ce, ga dadi amma kuma jikin sa ya gaya masa.” Inji Musa a cikin fushi.

Wani abu da PREMIUM TIMES HAUSA ta lura da shi, shi ne akwai gidajen da KEDCO ke tsallakewa ba ta kafa musu mota din, watakila saboda tsananin rashin karfin aljihun masu gidajen.

Kamar yadda Musa Kabuga ya ce ana shan wuta, PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa yanzu a Kano yawancin unguwanni na kwana cur da wutar lantarki. Haka da rana ma wutar ta na yini. Kenan tsadar ce ake kuka a kai.

Da ya ke tattaunawa da PREMIUM TIMES HAUSA kakakin yada labaran KEDCO na Kano da Jigawa da Katsina, Mohammed Kandi, ya bayyana cewa duk yadda jama’a ke kallon lantarki ba fa haka ya ke ba.

Ya ce jama’a na yin almubazzaranci da lantarki kafin su fara biya ta hanyar mita, saboda sun san karshen wata naira dubu 1,000 kacal ko 2,000 za su biya. Dalili kenan su ke kwana da firij da kwayaye a kunne.”

“Ka duba ko a shaguna da rana. Za ka ga shaguna a kulle, amma kwayaye na waje ba a kashe ba.” Inji Kandi.

Jami’in ya shaida cewa, su ma wuta a hannun hukumar raba hasken lantarki ta kasa su ke saye. “KEDCO ke bada wuta a jihohin Kano, Katsina da Jigawa. Ko kuma na ce mu ke kula da wadannan jihohi. To mun fara raba mita cikin 2016.”

“Lokacin da mu ka fara, mutane ba su yarda ana shiga cikin gidan su. Sannan kuma idan ma aka saka mita a cikin gida, ana burke ta. Shi ya sa mu ka ce to gara a rika kafa ta a kofar gidajen mutane kawai.”

“Daga lokacin da muka fara cikin 2016 zuwa yanzu mun raba,mita sama da dubu 150,000 a wadannan jihohi uku. Dama kuma tsarin da mu ka yi a karkashin amincewar hukumar raba wutar lantarki ta kasa shi ne a duk shekara za mu raba mita 100,000 a wadannan jihohi uku.”

Ya kara da cewa tun da aka kafa KEDCO a wadannan jihohi uku, har yau kamfanin asara ya ke yi, bai taba cin riba a duk wata ba.

Sai dai kuma ya ce a hankali idan mita ta yawaita a hannun jama’a, sannan ne za a fara fuskantar wani abu.

“Bai yiwuwa mutane su rika almubazzaranci da lantarki, sai karshen wata su biya naira 1000, wasu watannin ma ba biya za su yi ba. Yanzu kuwa idan ka na da mita, ka san cewa idan ka yi almubazzaranci, to kudin ka ne, lantarki ka ne.”

Idan ka lura, ai shekara 40 NEPA ta kwashe ta na kokarin samar da mita, amma abin ya gagara. Ka ga kenan mu muna kokari kenan. Domin a gaskiya idan babu mita, to lantarki ba zai yiwu a Najeriya ba.” Inji Kandi.

Yanzu dai masu amfani da mita sun shiga taitayin su, yadda har ta kai su na yawan duba balas din su na lantarki, tamkar yadda su ke yawan duba balas na kudin wayar salula din su.

Share.

game da Author