Sakamakon tsananin wahalar da aka fuskanta yayin cirar kudi domin yin shagulgulan karamar Sallah, PREMIUM TIMES HAUSA ta dan zagaya cikin Kano inda ta ji ra’ayoyin jama’a inda su ka Nina fushun su kan bankunan kasar nan.
Ba tun yau aka fara shan wahala a Kano da saura garuruwan Arewa ba idan an zo cirar kudi daga na’urar ATM. Kusan duk karshen wata haka masu ajiyar kudi kan yi cincirindo inda za a ga sama da mutane 100 sun yi layi su na jiran cirar kudi a bankuna daban daban.
Hakan kuwa na da nasaba ne da albashin da ake yi wa ma’aikatan gwamnati a karshen kowane wata. A wannan Sallah, masu karbar albashi sun yi katarin samun albashi tun ranar 22 da 23 ga wata. Hakan ya ba su damar cirar kudi ta hanyar yin amfani da katin ATM kwana daya kafin Sallah.
Saboda cinkoso a Kano tilas wasu suka rika cika motocin haya da kuma motocin su, su na garzayawa garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa domin su ciri kudi.
Malam Bashir Sani, malamin firamare ne, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa motar haya suka dauka shata, samfurin bas mai cin fasinja 10, suka je Dutse suka ciro kudi da katin ATM.
Ya ce ba don haka ba, to da bai san yadda zai yi tuwon Sallah ba. Shi da wasu da dama sun yi tir da karancin na’urorin ATM a Kano, duk kuwa da cewa Kano ce cibiyar hada-hadar kasuwanci a Kano.
Kabiru Salis kuwa shi da abokan sa Inuwa da Aminu Sulaiman, sun shaida wa Premium Times Hausa cewa ya kamata jama’a su nuna wa bankunan nan fushun su, ta hanyar zuwa bakin bankunan domin yi musu zanga-zangar lumana.
“Babu abin haushi sai ka kashe sama da awa biyu ka na bin layi, amma ana zuwa kan ka sai kudi ya kare, kai kuma ba ka da ko sisi a gida, kuma ba ka bai wa kowa ajiya ba.” Inji shi, ya ce haka ta faru da shi a ranar jajibiri.
Ba a wannan Sallah aka fara shan wahalar cirar kudi a bankuna ba. Wannan kuwa ya na da nasaba da karancin wuraren ATM sosai a Kano.
Yawancin kanana da manyan unguwannni kakaf babu wurin cirar kudi kuma babu rassan bankuna. Misali unguwanni irin su Karkasara, Hausawa, Sallari, Sheka da Darmanawa duk babu wurin cirar kudade.
PREMIUM TIMES HAUSA ta sake zagaya wasu bankunan washegarin Sallah inda ta fahimci yawan masu cirar kudi ya ragu a wasu wurare, a wadansu kuwa bai ragu ba, yayin da a wasu bankunan kuma babu kudi a akwatunan ATM din su.
Bankin GTB da ke da reshe a kan titin Zaria Road, ba ya rabuwa da cincirindon masu cirar kudi. Haka abin ya ke har washegarin Sallah.
Yayin da ATM na First Bank da ke Unguwa Uku, jama’a babu yawa, sai dai kuma hakan na da nasaba da rashin tabbas na saurin karewar da kudi kan yi ana cikin bin layi.
Dukkan bankunan da ke kan titin MTD irin su UBA, bankin Access Bank da Diamond, duk ba su rabuwa da jama’a kasancewa a ko da yaushe su na da garanti.
Premium Times ta zanta da wani ma’aikacin GTB wanda ya ce abubuwa hudu ko biyar ne da ke sa bankuna ba su yawan bude rassan cirar kudi a cikin unguwanni barkatai.
“Akwai dalilai na tsaro, akwai duba da cewa shin ya abin yake, akwai riba yin haka ko a’a? Sannan kuma shi kan sa kafa bankin ana la’akari ne da abubuwa da dama.”
Jami’in mai suna Gabriel, da ya nemi a sakaya mukamin sa, ya ce yawan ma’aikata ma da na dalilai na yawa ko karancin bankuna a unguwanni.
Ko ma dai me kenan, yawa-yawan jama’a na tafiya bisa ra’ayin cewa bai kamata bankuna su rika yi wa gari kamar Kano kwangen yawan rassan cirar kudi ta hanyar yin amfani da ATM ba.