• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Buhari Travelling

    Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

    An cika sansani uku fal da tubabbun ‘yan Boko Haram -Gwamna Zulum

    RUƊANI A APC: Gwamnan Neja, Bello ya ɗare kujerar Buni, Buhari ya bada umarnin Buni ya sauka daga shugabancin jam’iyyar

    IHU BAYAN HARIN SHIRORO: Gwamnatin Neja ta dakatar da haƙar ma’adinai a Shiroro, Munya da Rafi

    Barayi sun lalata tiransifoma 20 cikin makonni uku – Kamfanin Raba Wutar Lantarki

    SADAKA GUZURIN KIYAMA: Tsohon gwamnan da ya taya akanta jidar naira biliyan 84, ya yi wa malamai da ‘yan APC watandar shanu 370, ragunan layya 3,500 a Zamfara

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: INEC za ta raba kayan aiki marasa hatsari daga Owerri

    ZAƁEN GWAMNAN OSUN: Matsalar tsaro da guguwar sayen ƙuri’u ne abin da ya fi damun mu -INEC

    Ƴan sanda sun ceto ƙananan yara 50 da aka kulle cikin kurkukun wani coci a ƙarƙashin ƙasa, a Ondo

    ‘Na sadaukar da rayuwa ta ga Najeriya’ – Inji sojan da mahara su ka kashe a harin Shiroro

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    LMC ta ci tarar Kano Pillars, ta kori shugabanta, Jambul bayan ya gobza wa ‘Rafiri’ naushi a haɓa

    Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

No Result
View All Result

TATTAUNAWA: Yadda ake karatu a saukake a Jami’ar NOUN -Farfesa Adamu, Mataimakin Shugaban Jami’ar

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
July 4, 2018
in Rahotanni
0
NOUN students

NOUN students

Farfesa Abdalla Uba Adamu shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar da ake karatu daga gida, wato National Open University of Nigeria, NOUN a takaice. Kwanan baya tawagar PREMIUM TIMES da ta hada da Festus Owete, Ashafa Murnai da Ebuka Onyeji, sun yi masa takakkiya har ofis, inda su ka yi doguwar tattaunawa ta musamman da shi a kan batutuwa da dama da suka shafi jami’ar sa watta ta fi kowace yawan dalibai a fadin jami’o’in Afrika.

PT: Ka dade a cikin jami’a ka na koyarwa shekaru da dama tun ma kafin a nada ka shugabancin NOUN. Wane irin kallo ko kuma fahimta ka ke da ita dangane da karatu a irin wannan jami’a, a wancan lokacin?

Adamu: To a wancan lokacin dai ya na da wuyar gaske a amince da irin wannan tsarin karatun jami’a daga gida a gaba dayan tsarin karatun jami’o’i a kasar nan. Lokacin da aka kirkiro tsarin a cikin 1983, ba wanda ke da yakinin cewa zai samu karbuwa ko wani tagomashi kamar yadda ya karbu a yanzu. Ganin haka ne ma ya sa a ranar 25 Ga Afrilu, 184, sai gwamnatin mulkin soja ta lokacin ta soke shirin gaba daya. Wannan dakatarwa da aka yi wa tsarin ta bkanta mana rai sosai a lokacin. Ni fa na fara koyarwa a jami’a tun 1980. Shekara uku bayan nan nan a yi digiri na biyu.

Ni dama tuni tun a Ingila na gano irin wannan jami’a da ake karatu daga gida, a lokacin ban dauki abin da wani muhimmanci sosai ba. To bayan na dawo Najeriya cikin 1983, sai na ji za a kafa irin wannan jami’a a nan kasar. A zuciyata na ce, haba, wasan yara dai ku ke yi, saboda ban gama fahimtar abin sosai ba, ga shi kuma a wancan lokacin a kaset ake yin lacca sai a saida bidiyon idan an yi rikodin. Wani lokaci sai ka na cikin kallon bidiyon laccar sai a dauke wuta. Ga dai matsaloli nan daban-daban. Intanet kan sa a cikin 1991 ya zo Nijeriya.

An dawo da tsarin karatun a cikin 2003 bayan dakatar da shi da aka yi a cikin 1984. Ni dai a lokacin wani Dakta Aminu Ibrahim ne ya gayyace bayan ya ziyarce ni a Jami’ar Bayero, Kano ya ce na zo a farfado da jami’ar. Yayin da na je Lokoja, sai na ga ashe an kira wasu Farfesoshi su na can, inda muka hadu mu ka shafe wata daya mu na tsare-tsare.

Bayan mun kammala ne sai ko’odinetan shirin, Dakta Olugbemiro Jegede, wanda ya taba koyar da ni a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria, ya ja ni gefe ya ce min “Ina so ka zama shugaban tsangayar Ilmi na jami’ar, ni kuma na ce “a’a.” Har a lokacin ni ba ni da tabbaci ko yakinin tsarin ilmin, daga nan na rufe wannan shafi. To sai a 2016, kawai sai na ji labari a radiyo da kuma talbijin cewa ni ne Mataimakin Shugaban Jami’ar NOUN.

Dama kuma kafin sannan wani ya shaida min cewa wai su na tunanin aikawa da suna na. Ni kuma na ce masa don Allaha kada ka yi min haka mana, domin ba na so. Kafin sannan sau biyar ana yi min tayin shugabancin jami’a. An yi min a BUK sau biyu, an kuma yi min a Jami’ar Fasaha ta Wudil, Kano da kuma nan NOUN din a cikin 2010 a lokacin da wa’adin mulkin Jegede ya cika. To kwatsam yanzu kuma ga shi ina dai shugabancin na karbi tayin da aka sha yi min can a baya kenan. Na ce musu me ya sa ba ku cire suna na ba? Sai suka ce min ai har an rigaya an yi sanarwar nada ka.

PT: Idan ka yi waiwayen baya ka dawo ka kalli yadda jami’ar ta ke a yanzu, ko ka gamsu da matsayin da ta ke a yanzu?

Adamu: Ka ga dai kafin zuwa na, mutane ba su ma san yadda irin wannan tsarin karatun yake ba. Hatta su kansu hukumomin da ke sa ido a kan mu, ba su fahimce shi sosai ba. Su sun dauka wani karatu ne na je-ka-na-yi-ka, amma abin ba haka yake ba. Yanzu jami’ar ta tashi daga tsohon yanayin da ta ke ciki, komai yanzu da intanet ake gudanarwa. A yanzu sai a dauke ka jami’ar ta hanyar cika fom a wayar ka kai-tsaye. Mun kawo sabon sauyi, ilmi har a cikin aljihun ka, ba sai ka je aji ka yi zaman-dirshan ba.

PT: Amma idan ka kalli Najeirya, ba mu kai sauran kasashen da su ka ci gaba a fannin fasahar zamani ba. Mutanen karkara za su iya bibiyar zauren jami’ar ka ta intanet kuwa?

Adamu: Ai duk inda ka san ana samun intanet ta hanyar sadarwar MTN, Glo, Etisalat da Airtel, to ba su da matsalar bibiyar NOUN, tunda su na da intanet kenan. mu ba mu ma dauka cewa mutanen karkara ba za su iya samun mu ba ma, shi ya sa mu ka kafa cibiyoyin shiyya-shiyya na jami’ar har guda 75 a fadin kasar nan. Kenan duk irin kauyen da mutum ya ke za mu iya riske shi kenan.

PT: Dawo da jami’ar daga Lagos zuwa Abuja da ka yi, ya janyo ce-ku-ce. Me ye dalilin ka na dawo da jami’ar zuwa hedikwata a nan Abuja?

Adamu: Ba a taba cewa Lagos nan ne cibiyar wannan jami’a ba. Wannan jami’a ita kadai ce jami’a ta kasa baki daya. Saboda haka duk inda hedikwatar tarayya ta ke, can ya kamata a ce cibiyar jami’ar ta ke. Kuma haka dokar da ta kafa jami’ar ta bayyana. Lokacin da aka kafa jami’ar, sai aka ware wannan wuri da mu ke ciki a yanzu, nan a Kuci-goro, Abuja, aka ce nan za a yi mata hedikwata.

Aka ba ta ofishin fara aiki a Garki, wuri daya da ma’aikatar ilmi. A can aka fara gudanar da aiki. Lokacin da aka dawo da ci gaba da jami’ar a 2006, sai gwamnati ta ce gina jami’a a Abuja zai ci kudi sosai, tunda ga ginin ma’aikatar ilmi can a Lagos an taso an bar shi ba komai, to jami’ar ta tafa aiki can mana. To kun ji dalilin da ya sa NOUN ta fara a Lagos.

Kafin na zama mataimakin shugaba, ni ban ma san ashe gwamnatin Buhari ta gina wannan hedikwatar ba, sai da na je karbar takardar kama aiki, sannan na tambayi inda makarantar ta ke, aka ce min a Lagos, amma an gina mata hedikwata a Abuja, ko yanzu za a iya tarewa. Daga nan ni kuma na fara shirye-shiryen dawowa nan Abuja da cibiyar jami’ar.

PT: Dangane da kalubalen da NOUN ke fuskanta, ba ka ganin akwai bukartar kara wayar wa mutane kai kuwa?

Adamu: Kwarai kuwa, abin da mu ke kan yi kenan. Mu na yin iyakar kokarin mu. A kullum mu na watsa shirye-shiryen mu ta intanet. Duk wasu bayanai da ake bukata dangane da wannan jami’a, akwai su a intanet, cikin shafin mu na jami’ar. A wannan shekarar karatu mun dauki dalibai har 13,932.

PT: Me ya sa har yanzu ba a yarda daliban da su ka kammala NOUN su na zuwa aikin bautar kasa?

Adamu: Ai yanzu mun fito ka’in-da-na’in domin mu warware wannan matsala, mu na yin hira a jaridu, mu na sakin bayanai ga kafafen yada labarai. Sannan na sha zuwa Majalisar Tarayya a kan wannan matsala ta NYSC.

Lokacin da ka kafa makarantar cikin 1983, an bada muhimmanci ne a kan ma’aikata masu son zuwa karo ilmi ailahli su na kan aikin su. Yawancin su kuma duk manyan magidanta ne da suka haura shekarun zuwa aikin bautar kasa.

Ya zuwa tsakiyar shekarun 2000, wadanda ke son shiga jami’o’i ta hanyar jarabawar JAMB sun kara nunkawa. Daga cikin sama da milyan daya, 300,000 ne kadai za a iya dauka zuwa jami’a. To saboda wasu su na kokarin shiga jami’a amma ba su samu, sai suka yanke wa kan su wahala su ka ga gara ma su rika shiga NOUN kawai.

Sai ma suka gano cewa ashe yawancin mahajar karatu a NOUN duk farfesoshi ne ke tsara su. Sannan kuma za ka iya aiki ko ma a ina a lokaci daya kuma ka na karatu a NOUN. Wancan kallo da ake wa NOUN kamar wata jami’a ce da ake karatu ba na dindindin ba, wato part time, shi ne ya sa dokar NYSC ba ta yarda dan part time ya tai NYSC ba. Amma yanzu komai ya zo karshe, Majalisar Tarayya ta shigo cikin lamarin, ba da jimawa ba za a gyara dokar. Sannan duk wanda ya kammala NOUN, mu na ba shi satikfiket na yarje masa ba sai ya je aikin bautar kasa, NYSC ba, wato examption certificate.

Kamar yadda matsalar ta ke a NYSC, haka ma ta keg a masu kwas din ilmin shari’a, wadanda ba a bari su tafi karin karatu a Makarantar Shari’a, wato Law School. Yanzu duk rigimar na a gaban Majalisar Tarayya, kuma majalisar ta damu da wannan babbar matsalar, wadda ta sha alwashin cewa nan gaba kadan za ta yi dokar da za ta warware matsalar kowa ya huta, kowane dalibin NOUN zai iya zuwa bautar kasa, matsawar bai cika shekaru 30 ba, kuma wanda ya yi kwas na shari’a, daga nan doka za ta ba shi damar zuwa makaratantar shari’a kenan.

PT: Ya saukin karatu ya ke a NOUN?

Adamu: Naira dubu 41 kacal ake biya kudin shiga, amma daga nan, ilmi kyauta ne a NOUN. Idan dalibi zai dawo wani zangon kuma, wato session, zai biya naira dubu 13 kacal. Ka ga idan ka kwatanta da jami’o’in da ake biyan naira milyan daya ko milyan biyu a shekara, mu a kyauta mu ke bayar da ilmi kenan. Yanzu haka mu na da dalibai sama da dubu 400,000..

PT: Akwai lokacin da aka dauki ‘yan watanni shafin intanet na NOUN ba ya aiki, ya na rufe.

Adamu: Bayan na shigo, sai na gano cewa wai wani kamfani ne ke kula da shafin intanet na NOUN. Duk kudin da dalibai ke biya su na shiga jami’ar, a aljihun kamfanin ya ke tafiya, su za su dauki kashi 70, su bai wa NOUN kashi 30 daga cikin kashi 100. Ni kuma na ce ban yarda ba, na soke yarjejeniyar kwangilar da su.

Daga nan ne aka dauki wani lokaci ba mu da shafin fotal a intanet. Na ce ta-fi-nono-fari, gara mu kirkiro na mu da kanmu, tunda mu na da shashe musamman na ICT a NOUN, kuma kwararru ne, sun iya komai. Dalili kenan a yanzu an warware komai, mu ke gudanar da abin mu. Taskar bayanan mu ta intanet, wato portal ita ce nouonline.net. Amma sai wasu su ka kirkiro nounonline.net don su rika zambatar mutane. Tuni mun kai kara, mun wayar da kan dalibai da sauran jama’a kuma hukuma ta dauki mataki, kan mage kuma ya yawe.

PT: Ana korafin cewa ‘yan Kudu sun fi yawa a wannan jami’ar. Shin ya abin ya ke ne?

Adamu: Kamar dai yadda na sha fadi ne, abin ya na bukatar wayar da kai. Ka ga daliban jihar Sokoto su 648 ne kacal. Amma na jihar Delta su 33,000 ne. Ka san har yanzu wasu ba su karbi shirin ka yi karatu da kan ka ba, sun fi ganewa su zauna aji ga malam, ga allo ga kuma dalibi, ido-na-ganin-ido. Wannan kuma tsohon yayi ne, yanzu an ci gaba.

PT: Sai na ke ganin kamar har da dalilin cewa jami’ar ta dade a Lagos kafin kai ka dauko ta ka dawo da ita nan Abuja.

Adamu: Ba lallai wannan ne dalilin ratar da aka yi wa wani yanki ba. Maganar gaskiya akwai karancin wayar da kan jama’a a Arewa, wanda sai yanzu ne mu da muka shigo mu ke ta wannan kokarin.

PT: Idan haka ne, tabbas ba za a rasa irin wannan ratar ko a cikin ma’aikatan jami’ar ba.

Adamu: E akwai mana, ka san a baya ba kowane zai amince ya tafi Lagos ya zauna ya yi aiki ba. Ko ni ka ba ni aiki ka ce sai na zauna Lagos, a wancan lokacin, sai na ce maka ba na so.

PT: Mene ne kudirin ka a wannan jami’ar?

Adamu: Fata na shi ne na daukaka daraja da martabar NOUN sama da yadda na same ta. Sannan ina fatan na samar da yanayin da wanda zai gaje ni zai ji saukin tafiyar da shugabanci idan ya shigo.

Tags: Farfesa AdamuGarkiHausaJami’ar Ahmadu Bellojami’o’in AfrikaLabaraiMataimakin Shugaban Jami’arNOUNObasanjoShemeZaria
Previous Post

Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna – Inji El-Rufai

Next Post

Dalilai 5 da ya sa Jam’iyyar APC ta Kore Abdulmumini Jibrin

Next Post
Na yi nadamar maganganun da nayi akan Buhari – Abdulmumini Jibrin

Dalilai 5 da ya sa Jam’iyyar APC ta Kore Abdulmumini Jibrin

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • KOWA TA SA TA FISSHE SHI: Ƙoƙarin haɗewar LP da NNPP ya kakare, Peter Obi zai bayyana mataimakin takarar sa ranar Juma’a
  • ‘Da gangar aka bari ƴan bindiga suka kai harin gidan yarin Kuje, saboda na yi ta faɗin hakan zai auku – Mamu
  • Ƴan bindiga sun babbake cibiyoyin kiwon lafiya sun yi dalilin dole aka rufe wasu 69 a Katsina
  • Dala ta ƙara kekketa wa naira rigar mutunci daidai lokacin tsadar kayan abinci
  • Duk da tsananin hare-haren da ya darkaki Najeriya a kwanakin nan Buhari zai waske taro Dakar

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.