Kowa ya je yayi katin zama dan Kaduna – Inji El-Rufai

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da fara yin rijistar duk wani mazaunin Kaduna domin sanin iya adadin mutanen dake zama a jihar.

Kwamishinan Kasafin kudin Jihar, Mohammed Abdullahi ne ya sanar da haka ranar Laraba da ya ke yin na sa rijistan a Kaduna.

Mohammed ya ce gwamnati ta fitar da haka ne saboda ta san iya adadin mutanen da ke zama a jihar sannan kuma ta iya wadata mutanen jihar da ababen more rayuwa.

Gwamnati ta umurci duk wani wanda zai zauna a jihar da zai kai kwanaki 180 da ya tabbata yayi wannan rijista.

Ya ce wasu daga cikin dalilan yin wannan rijista shine domin gwamnati ta iya samarwa mutane ababen more rayuwa da kuma kara samar da tsaro a jihar.

Ya kara da cewa gwamnati na shirin samar wa mutanen jihar ababen more rayuwa wanda sai mutum yana da wannan shaida ne za iya amfana da wasu da ga cikin su.

Ya ce mutane su ziyarci wuraren da gwamnati ta kirkiro domin yin rijistan ko kuma a je ma’aikatar samarda da katin shaidan zama dan kasa domin a yi rijista.

Share.

game da Author