Idan har wannan kudiri ya tsallake mahawara a majalisa to zai zama an samar da sabuwar doka Kenan da zai hukunta duk wanda ya tsallake layi ya shiga gaban wani.
Kudirin na kira da a hukunta duk wanda yayi haka da zaman gidan yari har na tsawon wata shida.
Dan majalisa mai wakiltan jihar Kwara Abubakar Amuda-Kannike (Kwara-APC) ne ya kirkiro wannan kudiri.
Abubakar ya ce abin akwai ban takaici inda zaka ga mutane sun dade a layi sai wani ya zo kawai ya tsallakesu ya shige gabansu wanda hakan bai dace ba kuma ba dabi’ar mu bane.
Mafi yawa da ga cikin ‘yan majalisar sun nuna goyon bayansu akan hakan.
Yanzu dai kudirin ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.