Kungiyar ‘yan uwa musulmai wato ‘Shiite ta sanar cewa za ta gudanar da wata gangami na musamman gobe kamar yadda ta saba domin ranar Quds da mabiya akidar ke yi duk shekara idan ranar ta zagayo.
Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya yi kira ga mutane da su fito kwansu da kwarkwato don bin ayarin masu zanga-zangar gobe wanda suna yi ne domin nuna rashin jin dadinsu ga yadda kasar Israila ta mamye kasar Palastine.
Ibrahim Musa ya kara da cewa wannan gangami zai auku ne a manyan biranen kasa Najeriya. Bayan haka kuma ya yi kira ga gwamnati, a madadin duka mabiya akidar da ta bi umarnin kotu ta saki shugabansu Ibrahim El-Zakzaki.
“ Yau Kwanakinsa 588 kenan a daure duk da sakinsa da kotu ta ce anayi.”