A ranar Alhamis ne rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta cafke gungun wasu rikakkun ‘yan fashi da makami tare da yin garguwa da mutane a kan titin Jikamshi zuwa Yashe a cikin karamar hukumar Musawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ne da kan sa ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Katsiana. Kwamishina Abdullahi Usman, ya ce an cafke wadanda ake zagin su uku tun a ranar 18 Ga Yuni, 2017, a lokacin da ‘yan sanda suka yi gaggawar kai agaji a inda aka yi wani hadarin motoci a yankin na Musawa.
Ya ce wata motar fasinja ce ta gamu da wata motar da ta kwace wa direbanta, inda a nan take direban ya rasu, kuma fasinjoji da dama suka ji raunuka.
Ya ce an garzaya asibitin Musawa da wadanda suka ji raunukan cikin talatainin dare, “amma sai ‘yan sanda suka sha jinin jikin su, ganin cewa daya daga cikin fasinjojin da suka ji rauni akwai harbin bindiga a jikin sa.” Inji Kwamishinan ‘yan sanda.
Ya ci gaba da cewa wannan ya sa ‘yan sanda yin kwakkwaran bincike, inda suka rika shiga kauyuka suka tambayar ko akwai inda aka yi fashi, ko wani abu mai kama da haka.
Kamfanin dillancin labarai ya ruwaito kwamaishinan ya na cewa wasu kauyawa sun tabbatar wa ‘yan sanda cewa sun ji harbin bindiga kafin a yi hadarin.
“Yayin da mu ke gudanar da bincike, sai wata mota dauke da mutane uku ta zo wurin. Amma su na ganin ‘yan sanda sai suka nemi tserewa, amma aka yi gaggawar cafke su.
Ya ce wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun jima su na addabar jama’ar yankin. An kuma samu kwamfuta samfurin laptop, wayar selula har guda 19 a hannun su.
An kuma samu tsabar kudi naira dubu dari uku da hamsin da wasu kudaden kasashen waje a hannun su.
Kwamishinan ya kuma ce da aka kara matsa bincike, an same su wayar selular wani dan majalisar tarayya, wanda bayan ‘yan sanda sun tuntube shi, ya shaida musu cewa lokacin da aka yi garkuwa da shi a watannin baya ne wayar tasa ta salwanta.
Kwamishina Abdullahi ya ce nan ba da dadewa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.