Shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu ya ce muddum ba a zauna anyi maganar amince musu da kasar Biafra ba to lallai ba za a sake fitowa zabe a yankin ba kuma hakan zai fara daga zaben jihar Anambra da za ayi a watan Nuwamba.
Nnamdi Kanu ya ce burinsu su kafa kasarsu ne kawai kuma duk wanda ya ce ba haka ba zai mutu.
“ Babu wani dan yankin Biafra da zai yi zabe a 2019. Ba za muyi zaben shugaban Kasa ba, ba za muyi zaben yan majalisun tarayya ba da duk wani zabe da za ayi a lokacin sai an tabbatar mana da kasar Biafra.”
“ Saboda haka gwamnati ta yi shirin gina sabbin gidan yari domin sai dai a daure dukkan mu idan fa ba kasar mu aka bamu ba.”
Ya kara da cewa babu wani a kasar nan da ya isa ya hana kafuwar kasar Biafra, “kuma ina fadin haka ne domin kuje ku sanar da su domin a shirye muke mu sadaukar da rayukan mu akan hakan.”
Nnamdi Kanu ya fadi haka ne a wata sabuwar Bidiyo da ya saki da yake yin jawabi ga magoya bayansa a wani gida.